Jagoran Kyakkyawar Rayawar Addinin Musulunci.

ABUBUWAN DAKE CIKI

1.GABATARWAE
2.GODIYA
3. GODIYA

FASALIN FARKO

  • MA’ANAR KALMAR MUSULUNCIDA IMANI
  • KALMAR SHAHADA
  • SALLAH
  • ZAKKA
  • AZUMI
  • HAJJI

FASALI NA 2 (BIYU) BAYANI

  • BAYANI KAN SAMU (AKWAI)
  • BAYANI KAN BABU (RASHI)
  • BAYANI KAN TẠLAUCI
  • BAYANI KAN HALAL DA HARAM
  • BAYANI KAN SOYYAYA DA
    KIYAYYA.
  • BAYANI KAN SHUGABANCI
  • BAYANI KAN HALI NA GARI
  • KAMMALAWA.

GABATARWA

Bismillahir rahmanir rahim

Godiya ta cabbata ga Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai.

Tsaira da amincin Allah su tabbata ga
Manzon Allah sayyadina Muhammad
da Alayansa da sahabbansa da tabi’ai da
magabata wadanda ake koyi da su.

Ina farin cikin gabatar da wannan littafi mai din bin albarka mai suna “JAGORAN KYAKKYAWAR RAYUWAA ADDININ MUSULUNCI”
wanda dan uwanmu Alh Abdu Boyi ya
wallafa. Wannan littafi yana da mutukar
muhimmanci kwarai da gaske, saboda
ya kunshi abubuwa masu tarin amfani
ga rayuwa dan Adam baki daya,
musamnmam ma musulmi.

Gashi dai littafin karami ne, amma abinda yake cikinsa na darussa Allah yayi yawa dasu.
Saboda haka mutum zai iya
daukar wannan littaffi kamar abokin
hira, ko kuma abokin tafiya, yana
karantashi daga lokaci zuwa lokaci yana
tuna yadda ya kamata rayuwa tagari ta
kasance. Wani abin sha’awa da wannan litafin shine an rubutashi da Sauki da nutsuwa da fasaha wanda baba da yaro macce ko namiji zasu iya karantashi su kuma su amfana da shi .

Muna fatan Allah Ya saka masa da Alheri ya kuma bashi damar rubata wani littafin na gaba .Amin

FASALIN FARKO

MA’ANAR KALMAR MUSULUNCIDA IMANI.

Menene Musulunci?

Musulunci shine mika wuya ga Allah da
kuma dukkan abubuwan da Annabi
(S.A.W.) ya zo dasu. An gina musulunci
akan abubuwa guda biyar da ake
kiran su da SHIKASHIKAN MUSULLUNCI wato TAUHIDI SALLAH, ZAKKA, AZUMI da kuma HAJJI. Kafin muyi jawabi akan
wadannan shikashikan bari mu dan yi
tsokaci akan bambamci tsakanin
Musulunci da Imani.

Bayan yarda da amincewa da wadancan
shikashikan Musulunci guda biyar shi
kuma imani.

Menene Imani?

Imani shine yarda da Allah da Mala’ikunsa gaskiya ne Littattafan da ya aiko Attaura, Zabura, Injila, Alkur’ani da sauran wadanda bamu sansu ba dukkanninsu gaskiya ne da kuma manzaninsa waɗanda muƙa san sunayensu da waɗanda bamu san su ba dukkanninsu gaskiyane da kuma Ranar Lahira Gaskiyace Aljannah da wuta dukkanin su gaskiya ne Ƙaddara mai daɗi ko daci dukkaninta gaskiyace.

Dangane da bambamci

Tsakaninsu kuwa shine: Imani shi ne
sani da yarda da gasgatawar zuci,
shi kuwa Musulunci shine mika wuya gami da aikata ayyuka na zahiri, saboda
aikata wadannan ayyukan shi yake
tabbatar da samuwar imanin da yake
zuciya.

Tanan ne malamai suke cewa.
Dukkan mumini musulmi ne amma ba
dukkan musulmi yake mumini ba.
Don haka ya kamata musulmi mu tsaya
mu bi Allah domin komai dadewa
rayuwar duniya mai karewa ce, bin
Allah da Manzonsa shine zai sa mutum yasami A lahira da ƙuma shiga Aljannah .

Allah yasa mu dace,

Anan Zamu Tsaya Za mu tashi kashi na biyu da yardar Allah sai A sati na biyu.

Back to top button