Abdominal fat problems, massaging marks. Healthy lifestyle and sports activities concept stock photo...
Skinny fat woman figure in fitness clothes touches stomach. Abdominal fat and dieting concept. Massaging marks.
                    JIKIN DAN ADAM 
Gabatarwa: Abu-Unaisa

Mutane da dama sukan yi qoqarin rage qiba, za ma ka ji suna ta neman abin da za su sha don qibarsu ta ragu, ba shakka qiba wata hanya ce ta saduwa da cututtuka daban-daban, kamar su cututtukan zuciya, hawan jini, da sauransu, shi ya sa wadan da suka san ta za ka taras suna gudunta, haqiqa dole ne a kau da mummunan kitsen dake daskarewa a jiki, manyan abubuwan da ya kamata a yi amfani da su don kauce wa mummunar qiba har da man Kanumfari, don yana da mahimman abubuwan da za su taimaka akan haka.

 Sabo da yawan kasala kuwa Kanumfari kan ba da nasa gudummuwar, masamman in an yi masa hadi mai kyau, akan hada kanumfari, Hail wanda aka fi sani da Habbahan, gami da Na’na da ganyen shayin, in ya tafasu sai a sa zuma daidai gwargwado a sha, wasu suna aiki da shi a haka don qarfafa aikin qwaqwalwa ne, amma duk da haka yakan tattaro majinar da ta maqale a qirji.

  • Wasu kuma sukan yi aiki da shi ne kawai don sauqaqa radadin kai, wanda aka fi sani da ciwon kai, akan dan yi wani hadi da ake yi, a sanya man Kanumfarin a wani abu, a zuba gishiri a juya, sai a shafa a goshi, kamar damuwa da rikicewa da wani lokaci mutum kan sami kansa a ciki, ba tare da dalili ba sai ya hada shayin Kanumfari kawai don kau da gajiyar qwaqwalwa da ta jiki da ma Stress gaba daya, in ka sha shayin Kanumfari za ka ji qwaqwalwarka ta dawo sabuwa, ka ji ka rabu da duk abin da yake damunka, wani qari kuma yakan kawar da cutar hana barcin dare.

*  Kanumfari kan taimaka wa jakar fitsarin dake cikin mutum, yakan qarfafa ta, ya ba fitsarin damar fita cikin sauqi, in ma mutum yana da tsakwankwanin cikin qoda, Kanumfari kan kawar da shi cikin sauqi, ya ma kawar da abin da yake toshe jijiyar da take sada maraina da matafiyar fitsari, masana sun ce yakan qarfafa gabobin mahaifa ya tafiyar da al’adar mace kamar yadda ta dace.

* Za a iya amfani da shi don kawar da Inflammation don yana da Phenols da yawa, shi ya sa wasu magungunan da suka shafi kumburi da radadi za ka ji an ce ka dan watsa kanumfari, za a iya kawar da matsalolin Rheumatism da suran cututtukan gabobi.

* Kanumfari kan taimaka wajen tsara gwargwadon sukari a cikin jini, a shekarar 2006 aka yi wani Conference na Practical Biology, inda a qarshensa aka gano cewa abubuwan da aka sana’anta su da Kanumfari suna da qarfin da za su iya daidaita gwargwadon Insulin, su kuma rage yawan Glucose dake cikin jini, ban da wannan ma shi kansa Kanumfarin zai iya rage yawan mummunan Cholesterol da Triglyce wanda za su iya qara hatsarin yuwuwar kamuwa da cutar zuciya, masamman ga wadan da suke fama da cutar sukarin na biyu, masana suka ce masu fama da cutar sukarin za su iya amfana da kanumfarin wajen yin aiki da qwaya daya zuwa biyu a rana.

13) Maza ma sukan amfana da Kanumfarin, domin daya daga cikin matsalolin da maza suke fama da su har da saurin kawowa a yayin aiwatar da alaqar aure, shi kanumfarin yakan jinkirta kaiwar sha’awar namiji qololuwa ne, don da zarar namiji ya kai qarshe sai ka ga ya tunkudo ruwa, in sabon shiga ne sai barci, shi kuma Kanumfari yakan taimaka wa mazan, kenan macen da take fama da wannan matsalar ya kamata ta san hikimar da za ta yi, domin kar su yi jinkiri gaba daya, ita citta ma kawai ta ishe ta, shi kuma sai a dan kebance shi da Kanumfarin, sun ce idan shayin da aka yi shi da madara da Kanumfari yakan taimaka, har ma cututtukan maza na rashin haihuwa.

To kamar kullum, Kanumfari ma bai rasa nasa matsalolin, galibin abincin da muke ci, ko wanda muke sha shi ne yarammu suke ci su ma, sai dai su kanumfari bai tafiya da su sosai, yana da illoli masu yawa kamar yadda muka ambata a sama, lafiyarsu tana iya shiga cikin hatsari, cutar hanta ba qaramar cuta ba ce, kuma mun ambata cewa yakan magance tari, amma fa in aka yi aiki da shi ba yadda ya dace ba ba ko shakka za a dandana, hatta yawan tauna shi kai tsaye, ko wuce gona da iri wajen amfani da shi zai illata baki, dasashi, da haqora, shaqansa kai tsaye kuma da wasu suke yi, masana sun ce zai iya yin mummunan lahani ga numfashi da Inflammation din huhu.

Mata masu juna biyu ma ana ba su shawarar rage amfani da shi, sai dai ko in za su yi amfani da shi ne a matsayin kayan qamshi kadai a miya, ko wani abincin, masu ciwon haqori ya kamata su san cewa yakan kashe zafin ne kafin su ga likita, amma in suka ci gaba da aiki da shi to zai illata haqoran da dasashi gaba daya kamar yadda muka ambata, masu shan taba ko masu rayuwa da su a daki guda, matuqar suna turare su to zai yi kyau su ma su guji Kanumfari daidai gwargwado, in za a yi wa mutum aiki a asibiti shi ma kar ya yi amfani da shi don yakan tsinka jini, Kanumfari yana da matuqar amfani amma yana da qarfi sosai, shawara da likita ita ce hanya mafi dacewa don samun mafita.

Zamu cigaba insha Allah.

Rubutawa: Baban Manar.

Masu son kasancewa Damu ta shafin mu na Facebook sai su bi ta wannan link din dake kasa. 

Back to top button