A kwanakin baya ne dai fitaccen jarumin fina-finan Hausan nan wato Adam A Zango ya fito karara ya bayyana ficewarsa daga masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood.
Bayan fitarsa daga masana’antar, ya bayyana cewa zai fara cin gashin kansa ne, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.
Sai dai a wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya bayyana cewa a yanzu ya samar da hanyar da zai rinka fitar da sabbin fina-finansa ta intanet, inda masu kallo za su je su so siya .
A cewar Zango, babu yadda za a yi mutum ya kashe miliyoyin kudi wurin hada fim, kuma ya sake shi kara zube ko ya sa shi a Sinima, “da wuya kudaden su dawo”Da dama daga cikin ‘yan kannywood sun dade suna korafi kan satar fasaha ta yadda mutum zai kashe kudi ya yi fim amma daga baya wasu su sace fim din su sayar.
A lokacin da Zango ya fita daga masana’antar, ya ce ya yanke wannan hukuncin ne saboda zargin yadda ake shugabancin “kama karya da rashin hukunta mai karfi ko arziki, saboda kwadayi da son zuciya.”
Sai dai cewa bai yi karin haske ba sosai game da abin da yake nufi da fita daga kungiyar ba, ganin cewa akwai kungiyoyi da dama da suke cikin Kannywood, wata kila wannan hanya da ya fitar ta sayar da fina-finai ta intanet na cikin hangen da ya yi ya fita domin fara cin gashin kansa.