CIKAKKEN BAYANI AKAN TOILET INFECTION ALAMUNSA DA ILLOLINSA DA YADDA ZAABI AMAGANCHESI

 

Stomach ache. Asian women have abdominal pain, indigestion, gastritis, menstrual cramps, flatulence, diarrhea, distention, colon cancer, belly inflammation problem, suffer food poisoning, abdomen
close up of a people hand cleaning toilet seat

    TOILET INFECTION

Toilet Infection wata cuta ce da take samun mace da namiji, cuta ce wadda take a cikin mace da kuma gaban ta. Cuta ce wadda wani zai iya daukar ta daga wani, za’a iya daukar ta idan wata tayi fitsari a daidai wani wuri kema sai kije kiyi, za kuma ki iya daukar ta ta hanyar sharing pants da wadda take dashi. Haka kuma ana iya daukar shi a yayin saduwa (sex), mace zata iya gogawa namiji haka namijin ma zai iya gogawa mace shi.

Idan na kasa mata kashi dari tou fa 95% suna da wannan cutar. Cuta ce mai matukar wahalar magani ga wanda basu san yanda zasu magance shiba.

Tambaya anan itace:- shin me yasa mutanen da basu san miye toilet infection ba? Me yasa babu shi a baya?

Nikam a gani na hakan ya faru ne a dalilin yawan inserting da matan mu na yanzu keyi, matan da basu san miye cushe-cushe a gaba ba, yanzu ne abun yayi yawa. Idan ma zakiyi inserting din sai kisan abunda zakiyi dashi. Taya zaki mayar da vigina din ki tamkar wata bola? Duk abunda kikaga dama ki zuba a ciki kuma kisa ran zaki zauna lafiya? Hakan ba mai yiwuwa bane a gani na.

ABUBUWAN DA TOILET INFECTION YAKE HAIFARWA

1- rashin gamsar wa a yayin jima’i

2-rashin haihuwa

3-rikicewar al’adah

4-soshe-soshen gaba a cikin mutane, har wasu su ringa k’yamar ki da abun hannun ki.

5.kankancewar gaban namiji.

6.daukewar niima ga mata.

7.bushewar gaba.

8.kurajen gaba.

 ALAMOMIN TOILET INFECTION

1-fitar farin ruwa

2-rikicewar al’adah

3-kaikayin gaba

4-gaba ya ringa yin zafi a yayin yin fitsari

5-jin tsirar gaba ba tare da dalili ba

6-yin fitsari guntu-guntu.

HANYOYIN KARIYA TOILET INFECTION

1-Ki daina inserting ko wane irin magani a gaban ki, sai miski, duk wata kawa ko yar uwarki da zata baki wata shawara akan ki matsa wani abu yana karin ni’imah kar kiyi wallahi, ki bata shawara itama tayi kokarin dainawa.

2-ki ringa tsarki da warm water, (not too hot water dan kar ya sale ki…lol)

3-ki ringa inserting da miski a koda yaushe, yana warkar da wannan cutar sosai.

4-ki ringa shan maganin bature (tabs) saboda shi zai kashe miki na cikin.

5-ki jika ruwan lalle amma kar ki cika lallen da yawa, sai ki zuba zuma kadan a ciki, ki ringa shan cokali uku ko wace rana, shima zai kashe miki na cikin ki sosai. Saboda ko kinyi magani na kasan ki indai kina da na cikin tou akwai matsala, saboda ciwon yana nan.

HANYOYIN DA ZAKI BI YAYIN YIN MAGANIN TOILET INFECTION

1-ki wanke pants din ki da ruwan zafin da kika tafasa shi da gishiri, ki shanya su a rana har sai sun bugu sosai (idan so samu ne ma duka ki yarda su ki sake wasu).

2-duk maganin da zaki sha ya zamana mijin kima yana sha, idan kina da kishiyoyi suma susha, saboda ko kin sha magani kin warke aikin banza ne Indai suna dashi.

3-ki daina kwana da pant a yayin yin maganin shi, saboda ana bukatar iska ya yawaita shigar ki.

Annan zamu tsaya Sai Mu Tara lokaci na Gaba….

Post by Msz

Back to top button