Jagoran Kyakkyawar Rayawar Addinin Musulunci.
ABUBUWAN DAKE CIKI- MA'ANAR KALMAR MUSULUNCIDA IMANI
- KALMAR SHAHADA
- SALLAH
- ZAKKA
- AZUMI
- HAJJI
- BAYANI KAN SAMU (AKWAI)
- BAYANI KAN BABU (RASHI)
- BAYANI KAN TẠLAUCI
- BAYANI KAN HALAL DA HARAM
- BAYANI KAN SOYYAYA DA KIYAYYA.
- BAYANI KAN SHUGABANCI
- BAYANI KAN HALI NA GARI
- KAMMALAWA.
GABATARWA
Bismillahir rahmanir rahim Godiya ta cabbata ga Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai. Tsaira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah sayyadina Muhammad da Alayansa da sahabbansa da tabi'ai da magabata wadanda ake koyi da su. Ina farin cikin gabatar da wannan littafi mai din bin albarka mai suna "JAGORAN KYAKKYAWAR RAYUWAA ADDININ MUSULUNCI" wanda dan uwanmu Alh Abdu Boyi ya wallafa.FASALIN FARKO
MA'ANAR KALMAR MUSULUNCIDA IMANI.
Menene Musulunci? Musulunci shine mika wuya ga Allah da kuma dukkan abubuwan da Annabi (S.A.W.) ya zo dasu. An gina musulunci akan abubuwa guda biyar da ake kiran su da SHIKASHIKAN MUSULLUNCI wato TAUHIDI SALLAH, ZAKKA, AZUMI da kuma HAJJI.Dangane da bambamci
Tsakaninsu kuwa shine: Imani shi ne sani da yarda da gasgatawar zuci, shi kuwa Musulunci shine mika wuya gami da aikata ayyuka na zahiri, saboda aikata wadannan ayyukan shi yake tabbatar da samuwar imanin da yake zuciya.Tanan ne malamai suke cewa. Dukkan mumini musulmi ne amma ba dukkan musulmi yake mumini ba. Don haka ya kamata musulmi mu tsaya mu bi Allah domin komai dadewa rayuwar duniya mai karewa ce, bin Allah da Manzonsa shine zai sa mutum yasami A lahira da ƙuma shiga Aljannah .
Allah yasa mu dace, Anan Zamu Tsaya Za mu tashi kashi na biyu da yardar Allah sai A sati na biyu.
0 Comments