Stay connected with us Apkstore for Get Latest Update Now. apkstore.com.ng

Kano: Ba za mu lamunci shara ta mamaye birnin Kano ba - Dr Dahiru Muhammad Hashim.


Ba za mu lamunci shara ta mamaye birnin Kano ba – Dr Dahiru Muhammad Hashim”

  • Ma’aikatar kula da muhalli ta jihar Kano ta tabbatar da cewa aikin kawar da sharar zai gudana ne ƙarƙashin wani shirin haɗin gwiwa na kar-ta-kwana wanda zai tabbatar da cewa tulin sharar da ake fama ta shi a sassan jihar

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da wani gagarumin shirin yaƙi da matsalar shara da ke addabar sassan birnin.

Shirin na haɗin gwiwa da ma’aikatun ciniki da sufuri zai tabbatar da kwashe sharar da ta cika wuraren da ake tattara ta a kasuwanni da kuma unguwanni.

Jihar Kano na cikin jihohin da matsalar shara ke ci gaba da barazana a tituna da kuma unguwanni inda a wasu wuraren hayaƙin da ake kona bolar ke mummunar barazana ga jama’a.

Ma’aikatar kula da muhalli ta jihar Kano ta tabbatar da cewa aikin kawar da sharar zai gudana ne ƙarƙashin wani shirin haɗin gwiwa na kar-ta-kwana wanda zai tabbatar da cewa tulin sharar da ake fama ta shi a sassan jihar an kawar da shi cikin ƙanƙanin lokaci.

Kwamishinan ma’aikatar, Dr Dahiru Muhammad Hashim ya ce yanzu aiki an faro Shine daga kasuwanni zuwa cikin unguwanni.

“Akwai abubuwa da dama da gwamnati ba za ta ci gaba da lamunta ba don tabbatar da tsaftar muhalli da kare lafiyar al’umma.”

Bu-gu-da-kari Dr Dahiru Muhammad Hashim ya ce za su gayyato kamfanoni su zuba jari a harkar sarrafa shara, ta yadda jama’a za su daina kallon ta a matsayin shara, maimakon haka su kalleta a matsayin wani abu da za a iya samun arziki a cikinsa.

Post by Naziru Mai.

Download free APK files and Android apps from APK Store. Explore safe, verified, and updated Android applications across multiple categories...

Post a Comment