* Za a iya amfani da shi don kawar da Inflammation don yana da Phenols da yawa, shi ya sa wasu magungunan da suka shafi kumburi da radadi za ka ji an ce ka dan watsa kanumfari, za a iya kawar da matsalolin Rheumatism da suran cututtukan gabobi.
* Kanumfari kan taimaka wajen tsara gwargwadon sukari a cikin jini, a shekarar 2006 aka yi wani Conference na Practical Biology, inda a qarshensa aka gano cewa abubuwan da aka sana'anta su da Kanumfari suna da qarfin da za su iya daidaita gwargwadon Insulin, su kuma rage yawan Glucose dake cikin jini, ban da wannan ma shi kansa Kanumfarin zai iya rage yawan mummunan Cholesterol da Triglyce wanda za su iya qara hatsarin yuwuwar kamuwa da cutar zuciya, masamman ga wadan da suke fama da cutar sukarin na biyu, masana suka ce masu fama da cutar sukarin za su iya amfana da kanumfarin wajen yin aiki da qwaya daya zuwa biyu a rana. 13) Maza ma sukan amfana da Kanumfarin, domin daya daga cikin matsalolin da maza suke fama da su har da saurin kawowa a yayin aiwatar da alaqar aure, shi kanumfarin yakan jinkirta kaiwar sha'awar namiji qololuwa ne, don da zarar namiji ya kai qarshe sai ka ga ya tunkudo ruwa, in sabon shiga ne sai barci, shi kuma Kanumfari yakan taimaka wa mazan, kenan macen da take fama da wannan matsalar ya kamata ta san hikimar da za ta yi, domin kar su yi jinkiri gaba daya, ita citta ma kawai ta ishe ta, shi kuma sai a dan kebance shi da Kanumfarin, sun ce idan shayin da aka yi shi da madara da Kanumfari yakan taimaka, har ma cututtukan maza na rashin haihuwa.
To kamar kullum, Kanumfari ma bai rasa nasa matsalolin, galibin abincin da muke ci, ko wanda muke sha shi ne yarammu suke ci su ma, sai dai su kanumfari bai tafiya da su sosai, yana da illoli masu yawa kamar yadda muka ambata a sama, lafiyarsu tana iya shiga cikin hatsari, cutar hanta ba qaramar cuta ba ce, kuma mun ambata cewa yakan magance tari, amma fa in aka yi aiki da shi ba yadda ya dace ba ba ko shakka za a dandana, hatta yawan tauna shi kai tsaye, ko wuce gona da iri wajen amfani da shi zai illata baki, dasashi, da haqora, shaqansa kai tsaye kuma da wasu suke yi, masana sun ce zai iya yin mummunan lahani ga numfashi da Inflammation din huhu. Mata masu juna biyu ma ana ba su shawarar rage amfani da shi, sai dai ko in za su yi amfani da shi ne a matsayin kayan qamshi kadai a miya, ko wani abincin, masu ciwon haqori ya kamata su san cewa yakan kashe zafin ne kafin su ga likita, amma in suka ci gaba da aiki da shi to zai illata haqoran da dasashi gaba daya kamar yadda muka ambata, masu shan taba ko masu rayuwa da su a daki guda, matuqar suna turare su to zai yi kyau su ma su guji Kanumfari daidai gwargwado, in za a yi wa mutum aiki a asibiti shi ma kar ya yi amfani da shi don yakan tsinka jini, Kanumfari yana da matuqar amfani amma yana da qarfi sosai, shawara da likita ita ce hanya mafi dacewa don samun mafita.
Zamu cigaba insha Allah. Rubutawa: Baban Manar. Masu son kasancewa Damu ta shafin mu na Facebook sai su bi ta wannan link din dake kasa.
0 Comments