Sanarwar: Jami'ar Bayero Dake  Kano zata bawa, Gwanaye, Alarammomi da Almajirai kwas na tsawon watanni Takwas Kyauta.

 


Sanarwar: Jami'ar Bayero Dake  Kano zata bawa, Gwanaye, Alarammomi da Almajirai kwas na tsawon watanni Takwas Kyauta.

Jamiar Bayero dake Kano zata bawa, Gwanaye, Alarammomi da Almajirai kwas na tsawon watanni 8.

Wannan horo zai ba su zabin samun certificate a harshen Larabci ko kuma professional diploma. A karshe, zai kuma ba da damar samun gurbin yin Degree kai tsaye a jami'ar.
Ga wasu bayanai daga cikin sakon:


Bukatun: Mutum zai iya shiga wannan shirin idan yana da cikakkiyar haddar Alkurani, kuma yana bukatar a cike fom.


Matsayi: Wannan horon kyauta ne, sai dai dole ne mutum ya kai kansa jami'ar.


Cikin Shirin: Daga cikin shirin akwai zabin samun certificate ko diploma, sannan ana ba da damar ci gaba da karatu kai tsaye zuwa Digiri.


Cikakken Bayani: Domin samun karin bayani ko cike fom din, ana iya samun lambobin waya a cikin sanarwar ko kuma a tuntuɓi jami'ar ta hanyar zuwa Inna Plaza, jikin Sahad Store a kan titin Katsina.

Wannan horo kyautane, kawaii abinda ake bukata mutum ya kai kansa jamia.

Post a Comment

0 Comments

Android Apps