Amfanin Ayaba ga Lafiya Dan Adam
Ayaba na daga cikin 'ya'yan itace dake taimakawa halittun jikin mutum, musamman wajen tasirinta ga kuzarin 'ya'ya maza. Bincike ya tabbatar da cewar cin ayaba guda daya a kowacce rana zai matukar inganta lafiyar 'ya'ya maza ta hanyoyi da dama.
Akwai nau'ikan abinci da dama da suke kara lafiya da kuzari a jikin mutum, kuma ayaba na daga cikin waɗannan itatuwa da ke taimakawa sosai wajen inganta lafiya, musamman a fannin kuzarin 'ya'ya maza. Binciken kimiyya ya tabbatar da cewa cin ayaba guda daya a kowace rana zai inganta lafiyar maza ta hanyoyi da dama.
Ayaba tana da amfani wajen kula da lafiyar jikin mutum saboda tana cikin abinci mara maiko. Ta na taimakawa wajen cire kitse maras amfani daga jiki, inganta aikin kwakwalwa ta hanyar ƙara ƙarfin kwakwalwa, da kuma ƙara samar da sinadarin serotonin wanda ke sa mutum jin daɗi da walwala. A cikin ayaba akwai muhimman sinadarai irin su: vitamin A, B, E, PP, kalshiyum, ayon, sodiyom, maganeziyum, da fasfaros, waɗanda suke da matukar tasiri wajen inganta lafiyar kwakwalwa da kuma taimakawa wajen inganta halittun jima'i.
Sirrikan Amfanin Ayaba ga Namiji
Binciken masana ya tabbatar da cewa ayaba na hana hauhawar jini da kuma magance matsalolin uwar hanji. Sai dai, masana sun shawarci cewa akwai wasu yanayi da ya kamata mutum ya kaurace wa cin ayaba, musamman idan yana da matsalolin jinin da yake daskarewa, toshewar jijiyoyin jini a zuciya, ko kuma yana fama da cutar sukari. Saboda haka, kula da adadin ayaban da ake ci yana da muhimmanci.
Amfanin Ayaba guda 7 a Jikin Dan Adam
-
Rage Hawan Jini: Ayaba tana taimakawa wajen rage hawan jini musamman ga wadanda suke da matsalar hauhawar jini, saboda sinadarin potassium da take dauke da shi.
-
Asma: A wani bincike da aka gudanar, yara da suke cin ayaba guda a rana, suna samun kariya daga cutar asma.
-
Kare Cutar Daji: Amfani da ayaba a cikin shekaru biyun farko na rayuwar mutum yana taimakawa wajen hana kamuwa da cutar daji ta cikin jini. Sinadarin vitamin C a cikin ayaba na yaki da kwayoyin cutar daji.
-
Lafiyar Zuciya da Koda: Ayaba tana kunshe da sinadarai kamar potassium, vitamin C, da B6, wadanda ke taimakawa wajen yakar cututtukan zuciya da na koda.
-
Ciwon Sukari: Ayaba tana taimakawa wajen rage yaduwar ciwon sukari a cikin jini, ta hanyar sinadarin fiber da take dauke da shi.
-
Ciwon Ciki: Ayaba na magance cutar gudawa, saboda tana dauke da sinadarin potassium wanda ke taimakawa wajen daure jiki da kuma rage gudawa.
-
Kaifin Basira: Ayaba tana da sinadarin amino acid mai suna tryptophan wanda ke taimakawa wajen bunkasa kaifin basira da ƙarfafa kwakwalwa.
Ayaba na daya daga cikin kayan itatuwa da aka fi amfani da su a duniya, kuma ana noma ta a ƙasashe sama da 107.
A ƙasashe kamar Amurka, ana amfani da ayaba sosai, ciki har da haɗa ta da lemo da tufa. Saboda haka, ayaba na taimakawa wajen kula da lafiya da kuma inganta rayuwa a cikin al'umma.
Domin Karin bayani ana iya rubuta shi a comment section, kuma muna fatan za'a cigaba da kasancewa wannan wensite mai albarka domin samun post na ilmantarwa, fadakarwa dama sauransu,
Ana iya subscribe ta hanyar sa email don samun sabbin post na wannan website din shima akwai form na subscribe, mungode.