AMFANIN KANUNFARI
Kanunfari wani fitaccen sinadari ne wanda galibin mutane ke amfani da shi wajen girki da sha, haka kuma yana da wasu amfanin da ake amfani da shi wajen inganta lafiya da jin daɗi.
Ana amfani da itacen kanunfari, ganyensa, ko busasshen sa wajen sarrafawa domin biyan bukatu daban-daban a faɗin duniya. Ko da yake, galibin Larabawa da al’ummar ƙasashen Asiya sun fi amfani da shi.
Sirin Da Ke Cikin Shan Ruwan Kanunfari A Jikin Dan Adam
Masana harkokin lafiya sun bayyana amfanin wannan sinadari na kanunfari a rayuwar dan adam.
A tattaunawarsa da BBC, wani likita a Najeriya, Dr. Ibrahim Badamasi, ya ce ruwan kanunfari na da matuƙar amfani ga lafiya, domin yana ƙunshe da sinadaran da ke yaƙi da cututtuka da kuma ƙarfafa garkuwar jiki. Ruwan kanunfari na taimakawa wajen saurin narkewar abinci da hana cutar ulcer. Yana kuma taimakawa lafiyar haƙora, hana kumburin dadashi, da kuma fitar da jini.
Sannan, ruwan kanunfari na taimakawa wajen rage ƙiba da teɓa, magance jiri da cutar kwalara. Haka kuma, yana taimakawa wajen daidaita sukari a cikin jini da kuma inganta lafiyar hanta, saboda yana ƙunshe da sinadaran da ke hana lalata ƙwayoyin halitta.
Amfanin Kanunfari Ga Mata Da Maza
Binciken da masana kimiyya da dama suka yi ya nuna cewa kanunfari na ƙara wa mata da maza ni’ima. Kanunfari na da matuƙar amfani ga mata wajen inganta ƙwan haihuwa, kuma yana taimakawa wajen shawo kan matsalar rashin daukar ciki.
Kanunfari na bunƙasa isar wasu saƙonni ga ƙwaƙwalwa waɗanda ke motsa sha’awa ga mata da maza. Bugu da ƙari, kanunfari na ƙara wa mata kuzari lokacin jima’i, yana kuma taimakawa wajen rage tsufa.
Man kanunfari na taimaka wa mata wajen samun sauƙin ciwon mara a lokacin al’ada da taƙaita kwanakin al’adar.
Amfanin Kanunfari Ga Maza
Kanunfari na ɗaya daga cikin magungunan gargajiya da ke ƙara wa maza lafiya, domin yana ƙara yawan sanadarin ‘testosterone’ wanda ke tasiri wajen haɓakar gaɓoɓin saduwa na namiji.
Rashin isasshen sanadarin ‘testosterone’ a jikin namiji na iya haifar masa da matsalar rashin ƙarfin mazakuta, wanda kan rage masa ƙarfin sha’awar saduwa. Kanunfari kan inganta tafiyar maniyyin namiji. Yana kuma ɗauke da sinadarai da ke ƙara yawan maniyyin da namiji ke samarwa, wanda hakan ke da matuƙar amfani ga lafiyar maza.
Bugu da ƙari, kanunfari kan magance matsalar saurin fitar maniyyi ga namiji a lokacin saduwa, matsala da ke yawan faruwa ga maza saboda gajiya ko wasu matsaloli na daban.
Mai da ake samu daga kanunfari na ƙara ƙarfin miƙewar azzakari tare da inganta kwararar jini zuwa ga al’aura. Ana amfani da kanunfari wajen magance saurin fitar maniyyi ga namiji a lokacin saduwa ta hanyar haɗa shi da wasu ƙarin abubuwan, wadanda akan shafa a kan al’aurar namiji kafin saduwa.
Jeren Abubuwa 8 Da Kanunfari Ke Yi A Jikin Dan Adam (Daga Dr. Badamasi)
- Yana ƙunshe da sinadarai irin su Vitamin K, Fiber, Calories, Carbs, da Manganese.
- Yana ƙunshe da sinadaran da ke hana lalata ƙwayoyin halitta.
- Yana iya taimakawa wajen hana kamuwa da kansa ko sankara.
- Yana kashe kwayoyin cutuka.
- Yana inganta lafiyar hanta.
- Yana daidaita sukari a cikin jini.
- Yana ƙara lafiyar ƙashi.
- Yana hana kamuwa da ulcer.
Amfanin Kanunfari Ga Jikin Dan Adam Tare Da Yadda Ake Amfani Da Shi
Masana kiwon lafiya sun ce mutane na amfani da kanunfari wajen hana saurin fitar maniyyi a lokacin saduwa ko daɗin jima’i. Sai dai, ba a son a sha ko ci ya zarta iyaka. Idan aka yi amfani da shi sama da ka’ida, yana iya yin illa sosai.
Note
Ba a son a sha sama da itace hudu zuwa biyar a kowacce rana. Sannan ya danganta daga mutum zuwa mutum. Amma yana da kyau a tuntuɓi likita domin samun shawarwari kan yadda ya kamata a yi amfani da shi.
0 Comments