AMFANIN ZOGALE GOMA SHA HUDU (15) GA JIKIN DAN-ADAM
- Ana dafa ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi domin maganin Olsa (ulcer).
- Ana shafe danyen ganyen zogale akan goshi domin maganin ciwon kai.
- Ga wanda ya yanke ko ya sare ko wani karfe ya ji masa ciwo, zai shafa danyen ganyen zogale. Da yardar Allah jini zai tsaya.
- Ga mai fama da kuraje a jiki, ya hada garin zogale da man zaitun ya shafa.
- Ana sanya garin zogale akan wani rauni ko gembo domin saurin warkewa.
- Sanya garin zogale a cikin abinci yana maganin hawan-jini da kuma ƙara kuzari ga mutum.
- Ana dafa ganyen zogale tare da sa kanwa 'yar kadan domin maganin ciwon shawara.
- Ga mai fama da ciwon ido, zai daga ruwan danyen zogale a ido, haka ma mai fama da ciwon kunne.
- Macen da ke shayarwa ta dafa furen zogale da zuma dan karin nono.
- Wanda ke fama da yawan fitsari (cutar Diabetes) ya rinka shan furen zogale da citta kamar shayi.
- Idan aka tafasa furen zogale da Albasa aka sha kamar shayi, yana maganin sanyi.
- Haka ma cin danyen zogale yana maganin tsutsar ciki ga yara.
- A daka saiwar zogale da 'ya'yan kankana a sha da nono yana maganin tsakuwa ciki (Apendis).
- Haka kuma idan mutum yana fama da ciwon Aids, zogale na radadinshi ta hanyar shan ruwan dafaffen zogale.
- Ganyen zogale na da wadataccen sinadarin Vitamin D da sinadarin calcium domin karfin kashi da kwai mai karfi.
AMFANIN YA'YAN ZOGALE DA GANYEN TA
- Irin zogale na dauke da maganin antioxidants guda 46.
- Ganyen zogale yana da Vitamin C fiye da lemu sau 15.
- Ganyen zogale yana da Vitamin D sau 20 fiye da naman kashi.
- Ganyen zogale yana da furotin sau 25 fiye da yoghurt da madara.
- Ganyen zogale yana da potassium fiye da ayaba sau 10.
Nutritional Value of Moringa
Kowane sashi na ganyen zogale (ganye, iri, tushen) yana dauke da sinadaran gina jiki, bitamin da abubuwan gina jiki. Kowane bangare na ganyen zogale yana dauke da:
- Furotin
- Carbohydrates
- Fiber
- Fatty acids
Other Important Nutrients in Moringa:
- Ganyen zogale yana da wadatar calcium, phosphorus, potassium, iron, sodium da zinc.
- Ganyen zogale yana dauke da muhimman amino acids guda 7 da ake buƙata don nauyin jiki na yau da kullun da girma.
Benefits for Birds and Animals
- Ganyen zogale na kara yawan kwai da samar da nama da girma.
- Ganyen zogale na kara garkuwar jikin tsuntsaye, dabbobi, da kifi.
- Tare da ganyen zogale, za ku sami kashi 88 cikin 100 na samar da ƙwai da haɓaka girman kwai.
Vitamins and Minerals in Moringa for Animal Health:
- Ganyen zogale na da wadataccen Vitamin C, wanda ke taimakawa wajen rage damuwa a cikin dabbobi da tsuntsaye.
- Vitamin C yana taimakawa wajen haɓaka tsarin rigakafi da kare jiki daga cututtuka.
- Rashin sinadarin calcium na iya haifar da rashin girma da gurguwa, musamman ga broilers.
- Ganyen zogale na da wadataccen sinadarin Vitamin D da sinadarin calcium domin karfin kashi da kwai mai karfi.
Daga karshe:
Ganyen zogale na dauke da sinadaran gina jiki da yawa da suka hada da bitamin, ma'adanai, da amino acids. Wannan yana taimakawa wajen inganta lafiyar jikin mutum da na dabbobi, tare da magance cututtuka daban-daban. A amfani da zogale cikin abinci ko a matsayin magani zai iya kawo fa'ida mai yawa ga lafiyar jiki.
Allah yasa mu dace, Amin.
0 Comments