Sanata Natasha Akpoti da Sanata Akpabio
A ranar Alhamis, majalisar dattawa ta fuskanci hargitsi lokacin da shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ya umurci Sanata Natasha Akpoti, wacce ke wakiltar Kogi ta Tsakiya, da ta fice daga zauren majalisar. Wannan al'amari ya jawo cece-kuce a cikin majalisar yayin da Sanata Natasha ta ƙalubalanci umarnin shugaban majalisar, tana mai tsayawa kan 'yancinta na yin magana.
Sanata Natasha ta ce: "Ba na tsoronka!" tana bayyana cewa ba za ta daina magana ba, ko da shugaba Akpabio ya umurce ta da ta fice daga zauren. Wannan magana ta haifar da gardama a cikin majalisar, inda wasu 'yan majalisa suka shiga tsakani don kwantar da hankali da magance rikicin.
A cikin fushinta, Sanata Natasha ta zargi shugaban majalisar da yin zagon kasa ga Arewacin Nijeriya, tana cewa "Duk abinda zai kawo ƙaruwa a Arewacin ƙasar nan, wannan shugaban majalisa sai ya yi iya yinsa ya rusa abin saboda ba yankinsa ba ne." Ta bayyana cewa hakan yana nuna cewa Akpabio yana yawan kawo cikas ga ci gaban Arewacin Nijeriya.
Hargitsin ya samo Asali ne daga wani batu da Sanata Natasha ta kawo game da aikin yashe kogin Kwara, wanda a halin yanzu aka daina. Sanatar ta yi zargin cewa, shugaba Akpabio ya hana cigaban aikin ne domin hana Arewacin Nijeriya amfana daga ci gaban, saboda yana ganin aikin yana da alaka da yankin Arewa.
A karshe, wannan rikici ya jawo hankalin 'yan majalisar, kuma an yi ƙoƙari wajen warware matsalar da aka samu a lokacin zaman majalisar.
0 Comments