DA DUMI-DUMI: Babban Bankin Najeriya (CBN) Zai Kaddamar da Sabbin Dokoki Kan Ma'amalolin ATM Daga 1 Ga Maris, 2025
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da sabon tsari na cajin kudade da zai fara aiki daga ranar 1 ga Maris, 2025. Wannan tsarin zai shafi ma'amalolin ATM a cikin kasar. Ga cikakken bayanin sabon tsarin:
-
ATM Da Ke Cikin Banki (On-site ATMs): Za a caje Naira 100 kan duk wani ma'amala na cire kudi har N20,000.
-
ATM Da Ke Wajen Banki (Off-site ATMs): Za a caje Naira 100, tare da wani karin caji da ba zai wuce Naira 500 ba, kan duk wani ma'amala na cire kudi har N20,000.
-
ATM Na Bankin Da Aka Buɗe Asusu A Ciki (On-Us transactions): Idan kwastoma ya cire kudi daga ATM na bankinsa, ba za a caje komai ba.
Wannan sabon tsarin na nufin kawo daidaito a harkokin hada-hadar kudi a Najeriya, da kuma rage matsalolin da suka shafi cajin kudade akan ma'amalolin ATM. CBN na fatan wannan tsari zai inganta amfani da ATM a cikin kasar.
0 Comments