Stay connected with us Apkstore for Get Latest Update Now. apkstore.com.ng

Gwamnatin Bola Tinubu na shirin rage farashin kayan gini A Najeriya.


          Gwamnatin Bola Tinubu na shirin rage farashin kayan gini A Najeriya.

Gwamnatin Tarayya ta shugabancin Bola Tinubu ta kawo sabon tsari domin rage farashin kayan gini a  Fadi  Najeriya. Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnati za ta kafa cibiyoyin kera kayan gini a shiyyoyi shida na kasar.
Wannan mataki zai taimaka wajen rage dogaro da kayan gini daga kasashen waje da kuma inganta samar da gidaje masu araha.

A cikin wannan shiri, gwamnatocin za su yi amfani da cibiyoyin kera kayan gini domin samar da kayayyakin da za' a yi amfani da su wajen gina gidaje da sauran abubuwan more rayuwa. An yi nufin cewa wannan shiri zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, musamman ga matasa, wanda hakan zai bunkasa tattalin arzikin kasa baki daya.

Manufar kafa cibiyoyin kera kayan gini shi ne rage kudaden da ake kashewa wajen shigo da kayayyakin gini daga kasashen waje, wanda hakan zai saukaka yin gini da rage farashin gidaje a cikin kasar.

Wannan shiri na gwamnatoci zai ba da damar ci gaban masana’antu a Najeriya, wanda zai tabbatar da cewa kayan ginin na gida za su rika samar da ingantattun kayayyaki ga masu sha’awar gina gidaje a cikin kasar.

Ayyukan da ake sa ran samarwa ta hanyar wannan shiri za su kasance masu amfani wajen bunkasa tattalin arzikin kasar, rage rashin aikin yi, da kuma kawo ci gaba ga sassa daban-daban na Najeriya.


Download free APK files and Android apps from APK Store. Explore safe, verified, and updated Android applications across multiple categories...

Post a Comment