MALARIA : ABUBUWAN DA YA KAMATA KASANI AKAN CUTAR MALARIA


ABUBUWAN DA YA KAMATA KASANI AKAN CUTAR MALARIA

 MALARIA:-

Malaria cuta ce da ake samu sakamakon cizon sauro mai dauke da kwayoyin cuta da ke shiga cikin jinin mutum.

KWAYOYIN CUTAR DA SUKE KAWO MALARIA:

  1. Plasmodium falciparum
  2. Plasmodium vivax
  3. Plasmodium ovale
  4. Plasmodium malariae
  5. Plasmodium knowlesi

A Najeriya, mafi yawan lokuta na malaria ana samunsa ne daga Plasmodium falciparum, wanda ya sa ake amfani da maganin ACT don magance shi.

GA WADAN DA KE CIKIN ALAMUN MALARIA:

  1. Zazzabi
  2. Ciwon Kai
  3. Tashin Zuciya
  4. Amai
  5. Gudawa
  6. Ciwon Jiki
  7. Atini
  8. Dachin Baki
  9. Rashin Cin Abinci
  10. Rashin Karfin Jiki
  11. Kasala
  12. Rashin Jin Dadi

GA WADAN DA MALARIA ZAI KAMATA SU DAKE CIKIN HATSARI:

  1. Matar da ke dauke da ciki
  2. Yara Kanana
  3. Masu ciwon sickle cell (sicklers)

MALARIA A MACE MAI CIKI NA IYA KAWO:

  • Haihuwar macaccen jariri
  • Zubar da ciki
  • Haihuwar bakwaini
  • Kashe uwa da jaririnta baki daya

YADDA AKE GANIN MUTUM DA CUTAR MALARIA:

Ana iya gane malaria ta hanyoyi guda biyu, dukkansu na amfani da jini:

  1. RDT (Rapid Diagnostic Test)
  2. Microscopy (duba a cikin ruwan jini)

MATSALOLIN DA MALARIA KE KAWO (COMPLICATIONS OF MALARIA):

  1. Rashin jini a jiki
  2. Matsalar kwakwalwa
  3. Matsalar ciwon zuciya
  4. Matsalar huhu da oda
  5. Kumburi ko fashewar spleen (ƙwayar hanta)
  6. Saukar da suga (Hypoglycemia)

KARIYA DA KAMUWA DA CUTAR MALARIA:

  1. SPAQ (Sulfadoxine-pyrimethamine + Amodiaquine) – Magani ne da ake ba yara kanana daga watanni 3 zuwa 59 don kariya daga malaria. A Najeriya, kungiyoyin lafiya suna bayar da wannan magani a lokacin ruwan sama daga Yuli zuwa Oktoba, lokacin da ake samun yawan kamuwa da malaria.

Lura:

  • Yaron da ke da zazzabi ba a bashi SPAQ.
  • Yaron da ya sha septrin ba a bashi SPAQ.
  • Ba a haɗa SPAQ da wani maganin malaria ba.
  1. Fansidar (Sulfadoxine-pyrimethamine) – Magani ne da ake ba mata masu juna biyu domin kariya daga malaria. Ana ba mata maganin ne bayan wata hudu (16 weeks), sannan a sake ba su a tsakanin wata 20-22, sannan a ba su na uku a 26 weeks.

  2. Wasu magunguna da ake amfani da su domin kariya daga malaria sun haɗa da:

  • Proguanil
  • Doxycycline
  • Daraprim
  • Da sauransu
  1. Sauran hanyoyin kariya daga malaria sun haɗa da:
  • Shiga cikin gidajen sauro.
  • Daina barin ciyawa cikin gida.
  • Tsabtace muhalli da bayan gida domin kauce wa wurin zama sauro.
  • Kwashe shara daga gida a kai a kai.

MAGANIN ZAZZABIN CIZON SAURO:

Idan mutum ya kamu da zazzabin cizon sauro, yana da kyau a ziyarci asibiti domin samun cikakken gwaji daga likita, wanda zai ba da magani bisa ga gwajin da aka yi.

IDAN NAJI ZAZZABI, ZAN IYA SHAN COATEM?

A'a, ba a shan Coatem ko wani maganin malaria ba sai an tabbatar da cewa mutum na dauke da kwayar cutar malaria. Shan magunguna ba tare da tabbatarwa ba yana da illa. Mafi kyau, idan ka ga wadannan alamomi, ka tafi asibiti mafi kusa don a tabbatar da ko malaria ce ko wata cuta.

Zannah Mustapha Wakilu


Post a Comment

0 Comments

Android Apps