NIYEEDEP: Suna Cigaba da Turawa Wadanda Zasuci Gajiyar Wannan Shirin Sako Musamman Wadanda Sunka Bude Account Na Fidelity Bank

 


Rahoto: by Sani Abubakar 

Cikakken Bayani Kan Shirin Tallafin Manoma

Shirin tallafin manoma yana ci gaba da aikawa da sakonni musamman ga wadanda za su ci gajiyar wannan shiri. Wannan sakon yana kara tabbatar da mutum cikin shirin, don haka duk wanda ya samu wannan sakon, yana da muhimmanci ya tura adireshin Gmail dinsa wanda ya bude account din bankinsa zuwa ga mail din Bankin Fidelity.

Ga Wadanda Basu Samu Wannan Sakon Ba:

Idan ka kasa samun wannan sakon, kar ka damu. Za a tura maka sakon idan account din da ka bude ya dace da kalar account da ake bukata don shiga cikin wannan shirin.

Ga Wadanda Sun Bude Asusun a Keystone da Lotos Bank:

Har ila yau, ga wadanda suka bude asusu a Keystone Bank da Lotos Bank, ko da ba ku samu wannan sakon ba, kar ku damu. Kowanne banki yana da tsarin tantancewa na kansa wanda zai tabbatar da ingancin mutane da suka shiga cikin shirin.

A takaice, wannan sako yana tabbatar da cewa duk wanda ya bude account a bankin da ya dace kuma ya cika dukkan sharuddan da ake bukata, za a tura masa sakonni ko bayanai masu alaka da shirin. 

Post a Comment

0 Comments

Android Apps