Pi Network: Sun Tabbatar Da Wa'adin Ranar 28 ga Fabrairu Rana Ta ƙarshen Ga Masu KYC Verification.


 Pi Network

A cikin tsarin Pi Network, akwai matakin KYC (Know Your Customer) wanda ya zama wajibi don tabbatar da amincin masu amfani da tsarin. Akwai muhimmin sanarwa game da wa'adin KYC na ranar 28 ga Fabrairu wanda aka fitar domin masu amfani da Pi Network.

KYC da Wa'adin Ranar 28 ga Fabrairu

Wa'adin KYC na Pi Network na ranar 28 ga Fabrairu yana nufin cewa wannan wa'adi zai shafi kawai wadanda suka samu gayyatar KYC (KYC invitation ko KYC slot) amma basu kammala wannan mataki ba.

Wannan wa'adin bai shafi mutane da ba su sami gayyatar KYC ba ko kuma wadanda suka riga suka yi KYC amma kuma ba a kammala tsari ba (inda aka tsaya a matakin "pending"). Saboda haka, masu amfani da Pi Network da suka riga sun kammala KYC kafin wannan ranar ko wadanda har yanzu ba su samu gayyatar ba, ba za su shafa wannan wa'adi ba.

Me Ya Kamata Ku Sani

  • Wa'adin KYC na 28 ga Fabrairu zai shafi wadanda kawai suka samu gayyatar KYC amma basu kammala aikin ba.
  • Idan ka riga ka samu gayyatar KYC kuma har yanzu ba ka kammala ba, yana da muhimmanci ka kammala shi kafin wannan wa'adi, in ba haka ba za ka fuskanci wasu takunkumi ko kuma ragewa a cikin tsarin.
  • Wa'adin ba zai shafi wadanda ba su sami gayyatar KYC ba ko kuma wadanda suka kammala amma a cikin matakin pending.

A cikin wannan yanayi, yana da kyau ga dukkan masu amfani da Pi Network da suka samu gayyatar KYC amma basu kammala ba su dauki mataki cikin gaggawa domin guje wa rasa damar shiga matakai na gaba na tsarin Pi Network.

Post a Comment

0 Comments

Android Apps