Stay connected with us Apkstore for Get Latest Update Now. apkstore.com.ng

SANARWA!!! Mai alfarma Sarkin Musulmi Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III Mni CFR yayi Kira Da Afara Duba Saban Watan Ramadan 2025.

 


   SANARWA!!!      

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III Mni CFR, yana kira ga al'ummar Musulmi da su fita domin duba watan Ramadan a gobe Juma'ah, 28 ga watan Fabrairu, wanda yayi daidai da 29th ga watan Sha'aban. 

Wannan sanarwa na nufin cewa al'ummar Musulmi su fara duba watan Ramadan a wannan rana, wanda zai tabbatar da farawar watan azumi na Ramadan..Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alh.Muhammad Sa'ad Abubakar Cfr, Mni. Yau Yayi Taro Da Uwayen Ƙasa A Fadarsa Dake Sokoto.


Mai alfarma Sarkin musulmi Yayi Tsokaci Akan Harkar Polio Inda Yace Sun Yarda Da Wannan Allurar Polio Da Akeyi Domin Magance Wannan Cutar ta shan Inna da ke Addabar Al'umma.


Hakama Anba Sarkin Musulmi Tabbacin Akwai Wata Sabuwar Cuta data Bulla A Jahar Zamfara Amma An Samu Nasarar Maganceta.


Sarkin Musulmi Yayi Kira Ga Uwayen Ƙasa Dasu Zama Masu kula Akan Wannan Aikin na yaki da cutar Polio Domin tabbatar Da An bada Allura Yadda Yakamata.

 Sarkin musulmi ya kuma yi Kira Ga Al'umma Dasu guji Yada Karya Akan Sha'anin Ganin Wata Domin Akwai Masu Alhaki Da Kula da Wannan.

Daya Daga Cikin Yan Majalisar Sarkin Musulmi Kuma Galadiman Garin Sokoto Alh Aliyu Attahiru Yayi Tsokaci Inda Yace Akwai Foundation Na Sarkin Musulmi Wanda Ke bada Gudunmawa Sosai Domin Ganin Wannan Aikin Na Kiwon Lafiya, musamman yaki da cutar polio Ya Inganta Yadda Ake So.


Idan Allah ya sa, wanda zai iya ganin sabon watan, zai iya tuntubar daya daga cikin wadannan lambobi don samun karin bayani ko a taimaka musu:

  • 08037157100
  • 08066303077
  • 08099945903
  • 08067146900

Allah ya sa muna daga cikin bayin da zasu azumci wannan wata mai alfarma, kuma Allah ya sa muna daga cikin wadanda za su sami gafarar Allah a wannan watan mai albarka.

✍️ Alhamis, 27 ga watan Fabrairu, 2025.

Download free APK files and Android apps from APK Store. Explore safe, verified, and updated Android applications across multiple categories...

Post a Comment