SANARWA ZUWA GA MASU NEMAN SHIGA AIKIN 'YAN SANDA
Hukumar kula da aikin 'yan sanda ta Kasa (Police Service Commission) karkashin jagorancin DIG Hashimu Argungu (mai ritaya), tare da hadin gwiwar rundunar 'yan sandan Najeriya karkashin jagorancin IGP Kayode, za su yi daukar sabbin kuratan 'yan sanda.
Sanarwar ta bayyana cewa wannan karon ba za a cike takardun neman shiga aikin 'yan sanda ba saboda karancin lokaci. Saboda haka, za a dauki wanda suka taba neman shiga aikin, wadanda suka rubuta jarabawar Computer Based Tests (CBT) a ranar 5 da 6 ga watan Maris, shekarar 2024, amma ba su samu nasara ba. Daga cikin wannan rukunin za a diba wadanda suka cancanta.
Masu sha'awar shiga aikin 'yan sanda su shiga shafin yanar gizo wanda zai bude daga karfe 12 na yau a wannan adireshin:
https://apply.policerecruitment.gov.ng
Daga nan, za su iya buga (print) invitation slip din da zai kai su zuwa wurin gwajin lafiya (medical screening), wanda za a gudanar a asibitocin 'yan sanda dake Zonal Headquarters guda 17 a fadin Najeriya.
Za a fara gwajin lafiya nan da kwanaki hudu, wato daga ranar 26 ga Fabrairu, 2025, sannan za a kammala zuwa ranar 12 ga Maris, 2025. Dole ne wadanda ba za su iya halartar gwajin lafiya a wannan lokaci ba su fahimci cewa sun rasa damar shiga wannan zagaye na daukar aiki.
A taimaka wajen yada wannan sanarwa, domin ta isa ga 'yan uwa, musamman wadanda ke kauyuka.
Allah Ya ba da sa'a ga wadanda suka yi rajista.