KUNGIYAR YAN KASUWAR SINGA SUN YABA WA GWAMNATIN TARAYYA KAN FADUWAR FARASHIN ABINCI
Kungiyar yan Kasuwar Singa (SIMDA), da ke Kano, ta yaba wa Gwamnatin Tarayya kan inganta samar da abinci a kasar nan.
Shugaban kungiyar Barista Junaidu Zakari Mohammed ne ya yi wannan yabon a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a Kano.
Zakari ya ce matakan da gwamnatin tarayya ta dauka wanda suka haɗa da hana shigo da shinkafa da taliya da kuma noodles ya yi matukar tasiri a fannin daidaita farashin kayayyakin da ke kasuwa
“Muna yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa yadda ta yi watsi da shigo da kayan masarufi kamar shinkafa, taliya da makaroni, wannan ya yi dalilin saukar da farashin wadannan kayayyaki a kasuwa, wannan abin farin ciki ne.
“A yanzu mutane suna cikin farin ciki da cewa farashin abinci ya yi ƙasa, kuma da alamar babu fargabar zai sake tashi; kuma muna fatan zai kasance a haka har na wani dogon lokaci,” inji shi.
Daga nan sai shugaban ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar da yanayi mai gamsarwa don karfafa gwiwar masu samar da kamfanoni sarrafa abinci a kasar nan.
Hakan a cewarsa, zai kara yawan kayan abinci irin su taliya da indomi a kasar ta yadda zai ci gaba da karya farashin su a kasuwa.
Ya kuma bukaci gwamnati ta kara zage damtse wajen bunkasa harkar noma, gami da samar da ingantattun iri da za su samar da albarkatu masu yawa domin kara samar da abinci a kasar nan.
Daga nan sai Zakari ya yi kira ga gwamnati da ta kara daukar matakan inganta tsaro a kasar nan, domin bai wa manoma damar noma gonakinsu ba tare da fargaba ba, ya kara da cewa hakan zai kara inganta tsaro.
Ya kara da cewa "Muna sane da cewa tsaron rayuka da dukiyoyi ya inganta a kasar, amma muna kira ga gwamnati da ta kara kaimi wajen inganta lamarin."
Post by Sa'ed on Top....
0 Comments