Ƙungiyar MURIC mai fafutukar kare haƙƙin musulmi ta gargaɗi gwamnatin tarayya ta guji duk wani abu na muzgunawa Malam Nasir El-Rufai .

 


Takaitattun Labaran Daga Apkstore.....

Ƙungiyar MURIC mai fafutukar kare haƙƙin musulmi ta gargaɗi gwamnatin tarayya ta guji duk wani abu na muzgunawa Malam Nasir El-Rufai MURIC ta bayyana cewa muzgunawa tsohon gwamnan jihar Kaduna zai ɓata sunan gwamnatin shugaba Tinubu a idon duniya Wannan gargadi na zuwa ne yayin da ake raɗe-raɗin gwamnatin Najeriya na shirin kama Malam El-Rufai idan ya dawo Najeriya

 Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Ƙasa (NUT) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Ƙasa (NULGE), sun umarci malaman makarantun firamare da ke ƙarƙashin Sashen Ilimin Ƙananan Hukumomi (LEA) da su sake tsunduma yajin aiki.

 Haka kuma an umarci ma’aikatan ƙananan hukumomi shida na Babban Birnin Tarayya, da su dakatar da aiki daga jiya Alhamis, 13 ga watan Fabrairu, 2025, sakamakon rashin biyan mafi ƙarancin albashin Naira 70,000 da shugabannin ƙananan hukumomi suka yi.

📱Da Alamu gargaɗin ƙungiyar Ƙwadago ya fara tasiri: 

Kamfanin sadarwa na MTN ya ce kuskure aka samu shi yasa masu sayen data 15gb suka ga karin kashi 200 daga kudin data Ya kuma bai wa abokan huldarsa hakuri tare da basu tabbacin cewa suna sane da korafin da mutane ke yi.

Wata ɗalibar a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Bauchi, Faith Aluko Adesola, ta rasa ranta bayan da wata babbar mota ta murƙushe ta.

 Jami’in hulɗa da jama’a na makarantar, Alhaji Rabi’u Muhammad ne, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce Adesola ɗaliba ce da ke ajin farko (ND1) a Sashen Koyon Aikin Jarida na makarantar.

Babbar Kotun Jiha ta 5 a Gombe:, ƙarƙashin Jagorancin Mai Shari’a A.M. Haruna, ta yanke wa wani matashi mai suna Abdullahi Suleiman hukuncin sare masa hannu, bisa samunsa da laifin sare hannun wani yaro mai suna Khalifa Abubakar, ɗan shekara 14 da adda.

Lamarin ya faru ne a ranar 12 ga watan Fabrairu, shekarar 2022, a garin Moddibo da ke Ƙaramar hukumar Yamaltu Deba, a jihar ta Gombe lokacin wani bikin aure da ya rikiɗe ya koma rikici da misalin ƙarfe 11 na dare yayin da angon ya kori duk wanda ke wajen saboda hayaniyar da ta kaure.

A lokacin fitar jama’a daga wajen bikin, Abdullahi Suleiman, wanda ya fito daga ƙauyen Wajari, ya yi amfani da adda wajen tarwatsa jama’a tare da wasu matasa.

Khalifa Abubakar, wanda takalminsa ya faɗi a wajen gudu, ya tsaya don ɗauka, amma Abdullahi ya kai masa sara da adda har ya sare masa hannun dama gaba ɗaya.

Hukumar DSS a Nijeriya na son a riƙa tilastawa daliban da suka kammala digiri da mataki na farko su shiga aikin hukumar tsaro ta farin kaya.

  • Jami’an tsaro sun kama wani ma’aikacin lafiya da ake zargi da yi wa wasu ’yan bindiga da suka raunata magani a Ƙaramar hukumar Safana ta Jihar Katsina.


Wata babbar kotu a jihar Kano ta dage sauraren karar da aka shigar kan shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje da wasu mutane bakwai, bisa zargin cin hanci da almundahanar kudade har zuwa ranar 15 ga watan Afrilu.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa, zarge zarge takwas ne gwamnatin jihar Kano ta gabatar kan Ganduje, da matarsa Hafsat Umar.

Sauran wadanda ake kara sun hada da Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, da kamfunnan Lamash properties Limited, da Safari Textiles Limited da kuma Lasage General Enterprises Limited.


Wani matashi ɗan Jihar Yobe, Saifu Abdulrahaman, ya lashe kambun wanda ya fi ɗaukar hotuna masu yawa cikin sa'a ɗaya a duniya.

Matashin ya lashe kambun ne, ta hanyar ɗaukar hotunan dalibai 897 a sa'a ɗaya, domin wayar da kan mutane kan sana'ar hoto a Najeriya.


Mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro Nuhu Ribadu ya caccaki ƙasar Canada saboda ta hana wa babban hafsan sojojin Nijeriya Janar Christopher Musa da wasu manyan sojoji takardar visa domin shiga kasar.

  • Ribadu, wanda ke jawabi a wurin lackar da cibiyar horaswa kan sha'anin tsaro ta shirya a Abuja, ya bayyana matakin a matsayin cin fuskar Nijeriya.

Martanin da zuwa ne bayan da Janar Christopher Musa ya bayyana yadda hukumomin kasar Canada suka hana masa shiga kasar tare da wasu manyan jami'ai.

Hukumar Kwastam reshen Onne a Jihar Ribas tare da haɗin gwiwar ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro sun lalata kimanin kwantena 60 na kayayyakin da ba su da inganci da magungunan da aka shigo da su ba bisa ƙa’ida ba. Wanda ƙimar kuɗin su yakai Naira biliyan 100.

Gwamna Umaru Bago ya nada tsohon shugaban jam'iyyar APC, Jibrin Imam, a matsayin shugaban hukumar zaɓen jihar Neja Gwamna ya kuma nada tsohon sakataren APC, M.A. Liman da tsohuwar kwamishina, Amina Guar a matsayin kwamishinoni Jama'a da 'yan adawa sun nuna damuwa kan nadin 'yan jam'iyya, suna cewa hakan na iya kawo nakasu ga sahihancin zaɓen hukumar.


 Majalisar dattawa da majalisar wakilai na Nijeriya sun amince da kasafin kudin shekara ta 2025 wanda Shugaba Tinubu ya gabatar.

Kasafin da ya kai Naira tiriliyan N54.9.

Majalisar ta amince da kasafin ne bayan karɓar rhoton kwamitocin majalisa kan kasafin kudin da aka gabatar a jiya Alhamis.


An yi jana’izar fitaccen ɗan siyasar nan kuma Shugaban Hukumar Kwashe Shara na Jihar Kano (REMASAB), Alhaji Ahmadu Haruna Zago, a Ƙofar Kudu da ke Fadar Sarkin Kano.

 A yammacin jiya Alhamis . Ɗan zago ya rasu bayan doguwar jinya.

Dubban mutane ne suka halarci jana’izar fitaccen ɗan siyasar, daga ciki har da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, Sarkin Kano na 16, Sanusi Lamido Sanusi.


Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta bankaɗo ma'aikatan bogi 2,363 bayan aikin tantance ma'aikatan jihar da aka gudanar, tare da like hanyar zurarewar kudin gwamnati da suka kai naira miliyan 193.6 a kowane wata.

Gwamna Dauda Lawal ne ya kafa kwamitin karkashin jagorancin sakataren gwamnatin jihar Zamfara a watan Augustan 2024 da manufar tantance ma'aikatan jihar.

Wani bayani da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Idris, ya ce a yayin aikin an gano kananan yara 220 da aka sanya cikin ma'aikatan jihar kuma suke karbar albashi.


Shugaban kungiyar Northern Youth Forum Auwal Ibrahim Sansani ya kalubalanci sukar da kungiyar tuntuba ta Arewa wato ACF ta yi game da kalaman shugaban jam'iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje na cewa duk mai bukatar takarar shugaban kasa daga Arewa ya hakura har sai Tinubu ya kammala shekarunsa 8.

A wata sanarwar da Auwal Ibrahim ya fitar ya ce sun rasa me yasa kungiyar ACF din ta ke kin Shugaban kasa Bola Tinubu duk kuwa da kokarin da yake na dora Nigeria a turbar ci gaba.

" Dama kungiyar ACF ta dade tana nuna cewa ba zata goyi bayan Tinubu a zaben shekara ta 2027 ba, saboda a baya tsahon dakataccen shugaban kungiyar Mamman Osuman ya fito karara ya bayyanawa duniya cewa a 2027 ba za su goyi bayan duk dantkarar da ba daga Arewa ya fito ba, wanda hakan tasa kungiyar ta ce ta dakatar da shi daga mukaminsa". Inji Auwal Ibrahim Sansani 

Ya ce duk da kokarin da Tinubu ya ke na inganta tattalin arzikin Nigeria da dora kasar a turbar cigaba, amma sun fahimci tuni kungiyar ACF ta tsayar da matsayarta.


Wata Babbar Kotu a Abuja, ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar bayar da belin Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, wanda ke fuskantar zargin cin hanci da rashawa.


- Matsalar tsaro na kara karuwa a jihohin Kudu maso Yamma.

Gwamnonin yankin, sun yi zama na musamman don samawa al'ummarsu mafita. A karshen zaman, sun cimma matsayar kafa babbar rundunar tsaro ta hadin gwiwa.


Shahararren mawaki Tuface ya nemi auren mataimakiyar shugabar masu rinjaye ta majalisar dokokin jiha Edo

A wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta an ga yadda, mawakin Innocent Idibia, wato Tuface yake saka wa Natasha Osawaru zobe, wadda jikanya ce ga hamshakin mai kudin nan Gabriel Igbinedion.


- Tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, ya zargi Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ƙoƙarin hana shi magana sakamakon sukar manufofinta da yake yi.

  Yace bazai daina sukar gwamnatin ba har muddin bata sauya ba.

((wanne Labari ne yafi jan hankali ku?))


Post by Sa'ed A Sa'ed 

*Kano municipal*

Ina roƙon Allah yabawa Nijeriya shugabanni masu tausayi da adalci. Allah kahadamu da alkhairan wannan rana Ameen.

Mu yini lafiya.

Post a Comment

0 Comments

Android Apps