Yadda Zaku Iya Amfani Da Bawon Ayaba Don Wanke Hakoran Ku Dan Suyi Haske Sosai


Amfani Da Bawon Ayaba Don Wanke Hakoran Ku Dan  Suyi Haske Tara's.

Abin Mamaki: Da magani a gonar yaro amma baya ganin sa! Shin kun san cewa zaku iya amfani da bawon ayaba don wanke hakoran ku suyi haske sosai?

Wasu masana kiwon lafiyar hakora suna bada shawarar cewa mutum ya ringa amfani da bawon ayaba yana gogawa a hakoran sa na tsawon minti 2 a rana. Sunce yin amfani da bawon ayaba wajen gurzawa a hakora yana inganta lafiyar hakori da cire duk wani datti dake makale a jikin hakoran.

Wannan na iya zama abin mamaki ga wasu, amma a zahiri, za ku iya amfani da bawon ayaba don goge haƙoranku. Bawon ayaba yana dauke da sinadaran da ke taimakawa wajen inganta lafiyar hakora. Akwai wasu sinadarai a cikin bawon ayaba da suke da yawa, wadanda ke sanya shi mahimmanci ga hakoran.

YADDA ZAKA WANKE HAKORIN KA?

Idan ka tashi don wanke hakoran ka, samu ayaba cikakkiya (nunanniya) wacce ba tayi ja ba kuma ba rubabiya ba.

Ga matakan da za ku bi domin goge hakoran ku:

  1. Samu Ayaba Mai Kyau:
    Samu ayaba wacce take mai kyau, ba wadda ta lalace ba. An fi son ayaba mai girma wacce ta nuna inganci, domin wannan yana dauke da sinadarai masu kyau da za su taimaka wajen kula da lafiyar hakora.

  2. Shafa Bawon Ayaba A Jikin Hakoran Ka:
    Ku goga bawon ayaba na tsawon minti goma a hakoran ku, daga na sama zuwa na kasa. Ku tabbata cewa sinadaran dake cikin bawon ayaba sun ratsa dukkan sassan hakoran ku, musamman wuraren da suke da datti ko launin shudi.

  3. Goge Hakoran Da Burushi:
    Da zarar mintuna goma sun cika da shafa bawon ayaba, ɗauki burushi busashe ka goge hakoran naka da shi. Wannan zai taimaka wajen cire duk wani datti ko saura daga bawon ayaba.

  4. Yi Haka Kowace Rana:
    Abu mai wuya ka ga sauyi a lokaci guda, amma idan ka jure yin hakan na tsawon sati biyu, za ka yi mamaki yadda hakoran ka za su canja. Hakoran za su yi fari, suyi haske, kuma suyi ƙwari.

A Takaice ...

Duk da cewa amfani da bawon ayaba wajen wanke hakora na iya zama sabon abu, yana dauke da sinadaran da zasu iya inganta lafiyar hakora da kuma sanya su suyi haske. Idan aka aiwatar da wannan hanyar na kullum, zai yiwu ga mutum ya sami kyakkyawan sakamako.

Post a Comment

0 Comments

Android Apps