Gabatarwa.
Da sunan allah mai rahama mai jin kai, dayin salati ga fiyayyen halitta annabi muhammad tsira da amincin allah sutabbata agare shi, shida sahabbansa, da mutanen gidansa tsarkaka, da wadanda suka bisu da kyautatawa har izuwa ranar tashin alkiyama.
Manzon allaah [s.a.w.] yace: lallai allaah bai saukar da wata cutaba face yasaukar da magani maganinta’’
bayan haka, dalilin rubuta Mai Suna [amfanin ya’yan’ itace ajikin dan adam] shine: don musan amfani da kuma maganin abubuwanda mukeci yauda kullum sukeyi ajikin mu.
sanin amfaninsu zai kara mana himma wurin amfani dasu don naiman lafiyarmu.
Amma kusani wadannan abubuwa da zan kawo mana, wasune suka bincikosu awurare maban-banta, sai ni kuma naga amfanin su, sannan sai nayi tunani akan cewa mai zai hana natarosu awuri guda daya ta yadda al’umah zata amfana dasu, batare da sai sun wahalaba wurin nemo amfanin suba.
ina addu’ah allah yasa wannan littafi ya zamo mai amfanar al’umah baki daya.
ina fatan duk wanda yaga wani kuskure zai gyaramin saboda allah.
AMFANIN GYADA AJIKIN DAN ADAM.
Gyada Na Taka Rawa sosai wajen Gina jikin da Adam, da kuma Bashi kariya da kuma kara mishi lafiya. Mafi yawa daga cikin mutane ba su da masaniya kan amfanin da gyada ke yi a jikin mutum.
Gyeda da muka raina tana dauke da sinadarai na nutrition kamar haka:
- Carbohydrate
- Calcium
- Phosphorus
- Iron
- Thiamine (B1)
- Riboflavine(B2)
- Niacin
- Calories
- Protein
- Fat
Tabbas Akimiyance, Masana Sun Tabbatar da kasancewar Sinadaran da jikin dan adam ke bukata suna kunshe Acikin Gyada, Irinsu:
Vitamin ‘’E’’
CALCIUM,
PHOSPHORUOS Da Dai Sauransu.
Haka kuma Hukumar Abinci Ta Duniya wato [FAO] Ta Tabbatar Da cewa Gyada Itace Nau’in Abinci Na Goma Sha uku [13] Asikelin muhimman Abincin Duniya, kuma gyadace ta hudu cikin Nau’ukan Abinci da Ake Samun man girki, wannan Ingancin Na Gyada Amatsayin kayan Abincin yasa AL’umar Duniya suke bukatarta sosai, haka kuma yasa kusan babu inda ba’a Amfani da ita Acikin duniya saboda haka zaku iya soya gyada ko dafata ko cinta danya, ko zubata Amiya Aci, sannan Atatseta Afitar da mangyada, Duk da haka Amfaninta Nanan. Cuta da magani Alikitance.uwa marasa kyau Ajikin mutum.
Amfanin gyeda a jikin dan Adam:
> Yana bunkasa girman jikin mutum musamman yara domin yana dauke da sinadarin ‘Protein’.
> Gyada na gyara fatar jikin mutum da hana saurin tsufa saboda akawai sinadarin ‘vitamin E’ a ciki.
> Gyada na faranta wa mutum rai musamman masu yawan fushi.
> Gyada na kare mutum daga kamuwa da cutar bugawan zuciya.
> Gyada na dauke da sinadarin ‘vitamin B3’ wanda ke taimakawa wajen hana mutum mantuwa.
> Yana dauke da sinadarin ‘Phylosterols wanda ke kare mutum daga kamuwa da cutar daji.
> Yana kuma kare mutum daga kamuwa da cutar siga.
> Ana samun sinadarin ‘Folate’ wanda ke bunkasa kiwon lafiyan mata masu ciki.
> Gyada na kara karfi a jiki.
Lafiya Uwar jikii...
post by Musa Isah Mukutar .