Gabatarwa.
Da sunan allah mai rahama mai jin kai, dayin salati ga fiyayyen halitta annabi muhammad tsira da amincin allah sutabbata agare shi, shida sahabbansa, da mutanen gidansa tsarkaka, da wadanda suka bisu da kyautatawa har izuwa ranar tashin alkiyama.
Manzon allaah [s.a.w.] yace: lallai allaah bai saukar da wata cutaba face yasaukar da magani maganinta’’
bayan haka, dalilin rubuta Mai Suna [amfanin ya’yan’ itace ajikin dan adam] shine: don musan amfani da kuma maganin abubuwanda mukeci yauda kullum sukeyi ajikin mu.
sanin amfaninsu zai kara mana himma wurin amfani dasu don naiman lafiyarmu.
Amma kusani wadannan abubuwa da zan kawo mana, wasune suka bincikosu awurare maban-banta, sai ni kuma naga amfanin su, sannan sai nayi tunani akan cewa mai zai hana natarosu awuri guda daya ta yadda al’umah zata amfana dasu, batare da sai sun wahalaba wurin nemo amfanin suba.
ina addu’ah allah yasa wannan littafi ya zamo mai amfanar al’umah baki daya.
ina fatan duk wanda yaga wani kuskure zai gyaramin saboda allah.
AMFANIN LEMON TSAMI AJIKIN DAN ADAM
AMOSARI: Yana Amfani wajen kawar da Amosarin kayi.QARNI: Ana Amfani dashi wajen kawar da karnin kifi.
GYARAN FUSKA: Yadda ake Amfani dashi shine: za’a Rabashi gida Biyu, Rabin sai Agoge fiska dashi Na Yan’ wasu lokuta, sannan Akula kar yakai ga Idanu, kar Ashafa Ashiga Rana sai Ankwanke.
DATTIN HAKORI: Ayi Amfani da Abun wanke baki da Ruwan lemon tsami Awanke Hakorin, zasu fita tas, Amma kada Ayawantayi Akai Akai. Don zai Iya Raunata hakori.
WARIN KASHI [HAMMATA]: Ana Iya shafa shi Ahammata domin zai gusar da warin hammatar da wuri.
RAUNI [CIWO]: Sabon Raunin da bai wuce Hankaliba, da zarar An matsa mai Lemon tsami zai kame yawarke, Ammafa yana da zafi sosai.
AMFANIN RAKE AJIKIN DAN ADAM GUDA [10] GOMA.
Yana kara karfin hakori da kasusuwan jiki, Akwai sinadaran calcium da phosphorus wanda suke matikar taimakawa wajen kara karfin kashi da hakori.
Yana Taimakawa wajen Cire warin baki da Rubewar hakora.
Yana Taimakawa wajen Narkewar Abinci.
Sinadarin Potassium Dake cikin Rake
yana Taimakawa wajen Rage gubar ciki, wanda wannan Gubar Itace Take Hana Abinci yanarke da wuri Acikin mutum.
Yana Yaki da Cutar Daji ta Mama, Saboda Akwai Sinadarin flavonoids Dayake Hana yaduwar kwayoyin Cutar Daji Musamman Amaman mata, kuma Akwai Sinadarin potassium, calcium, Iron, Magnessium da suke kara karfafa wannan kariyar.
Shi warakane daga ciwo mai Radadi Na makoshi, Akwai yawaitar sinadarin Vitamin C da yake kawo waraka daga ciwon makoshi mai Radadi.
Yana taimakawa wajen Rage Nauyin jiki.
Yana kara Ruwa Ajiki.
Yana Taimakawa mata masu Juna Biyu, yana dauke da Sinadarin Folic Acid ko kuma B9 wanda yake bayar da kariya ga Haihuwar jarirai masu nakasash-shen Baya.
Post by TTech.....