Bikin Karamar Sallah: Hotunan Sallar Idi Daga Masallacin Ƙofar Mata Na Kano
Mai martaba sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sunusi na biyu ya ja jagoranci Sallar wadda Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir da sauran manyan muƙarraban gwamnatin jihar da ɗumbin al'ummar suka halarta.
Isowar Mai Girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf kenan zuwa Babban Masallacin idi dake unguwar kofar Mata, Cikin birnin Kano.
Waɗannan da kuke gani ba kowa bane face zunzurutun Matasa Mata da Maza ke tururuwar nunawa mai girma Gwamna soyayya.
A yayin isowar dai na mai girma Gwamna al'umma na tururuwar nanata goyan bayansu da amincewar su da nuna maradin akan Abba gida gida sai yayi hudu ya kara hudu (4+4)