Stay connected with us Apkstore for Get Latest Update Now. apkstore.com.ng

𝗔𝗣𝗣𝗟𝗜𝗖𝗔𝗧𝗜𝗢𝗡𝗦 𝗚𝗨𝗗𝗔 𝗚𝗢𝗠𝗔 (𝟭𝟬) 𝗗𝗔 𝗭𝗔𝗦𝗨 𝗔𝗠𝗙𝗔𝗡𝗘 𝗞𝗨 𝗜𝗗𝗔𝗡 𝗞𝗨𝗡𝗔 𝗛𝗔𝗥𝗞𝗢𝗞𝗜𝗡 𝗢𝗡𝗟𝗜𝗡𝗘.

 

Barka da zuwa wanan shafin namu mai albaraka .

Yau ma haka mun zo mu ku da wani saban topic Wanda da mutane da yawa sun Riga da sun San shi wasu kuma basu San shi ba.

 𝗔𝗣𝗣𝗟𝗜𝗖𝗔𝗧𝗜𝗢𝗡𝗦 𝗚𝗨𝗗𝗔 𝗚𝗢𝗠𝗔 (𝟭𝟬) 𝗗𝗔 𝗭𝗔𝗦𝗨 𝗔𝗠𝗙𝗔𝗡𝗘 𝗞𝗨 𝗜𝗗𝗔𝗡 𝗞𝗨𝗡𝗔 𝗛𝗔𝗥𝗞𝗢𝗞𝗜𝗡 𝗢𝗡𝗟𝗜𝗡𝗘


𝟏. 𝐂𝐚𝐩𝐂𝐮𝐭:Apk

Ana amfani da wannan application wajen hada videos, ko hada hotuna zuwa video, domin tallata abun siyarwa ko don ɗorawa a (social media handles) don samun followers ko likes.


𝟐. 𝐂𝐚𝐧𝐯𝐚:Apk Download 

Tana amfani da (𝗗𝗮𝘁𝗮 𝗖𝗼𝗻𝗻𝗲𝗰𝘁𝗶𝗼𝗻) Kuma ana amfani da ita wajen haɗa flyer, logo, documents, letters, thumbnail, banner ID card, Business Card, video, da editing na hotuna da dai sauransu, amma Canva ta nada (𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗩𝗲𝗿𝘀𝗶𝗼𝗻 𝗱𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗣𝗿𝗲𝗺𝗶𝘂𝗺 𝗩𝗲𝗿𝘀𝗶𝗼𝗻). Canva tana da saukin fahimta kuma tana ɗauke da Free Template da zaku iya customizing zuwa naku.

𝟑. 𝐏𝐢𝐱𝐞𝐥𝐥𝐚𝐛:Apk 

Shima kamar Canva application yake amma shi baya amfani da Data Connection zaka iya buɗe shi ko baka da Data a wayarka, ana haɗa abubuwa dayawa dashi wanda suka danganci (𝗴𝗿𝗮𝗽𝗵𝗶𝗰 𝗱𝗲𝘀𝗶𝗴𝗻).

𝟒. 𝐂𝐚𝐦𝐒𝐜𝐚𝐧𝐧𝐞𝐫:Apk Download 

Ana amfani da wannan application wajen scanning na takardu ko wani muhimmin abu, kuma ana iya amfani dashi wajen kwafan rubutu da yake jikin hoto ko takarda ya koma (𝗱𝗼𝗰𝘂𝗺𝗲𝗻𝘁 𝘁𝘅𝘁).

𝟓. 𝐙𝐀𝐫𝐜𝐡𝐢𝐯𝐞𝐫:Apk Download 

Wannan application yana amfani wajen (𝗲𝘅𝘁𝗿𝗮𝗰𝘁𝗶𝗻𝗴 𝗻𝗮 𝗳𝗶𝗹𝗲𝘀) ko nace (compressing) daga (Zip Files) zuwa hotuna, video da sauransu. Sannan ana amfani dashi wajen haɗe (𝗙𝗶𝗹𝗲𝘀) guri guda, Misali kamar Kanada videos guda goma, zaka iya haɗe su guri daya su zama (Zip File) da wannan application.

𝟔. 𝐈𝐧𝐬𝐡𝐨𝐭:Apk 

Ana amfani da wannan application wajen haɗa video ko editing na wani video zuwa wani abu daban, kuma ana haɗa hotuna izuwa video a cikinsa. Sannan yana da Features dayawa kamar (𝗳𝗿𝗮𝗺𝗲 𝗿𝗮𝘁𝗲, 𝗿𝗲𝘀𝗼𝗹𝘂𝘁𝗶𝗼𝗻, 𝗱𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗴𝗶𝗿𝗺𝗮𝗻 𝗖𝗮𝗻𝘃𝗮𝘀 𝗻𝗮 𝘃𝗶𝗱𝗲𝗼).

𝟕. 𝐆𝐫𝐚𝐦𝐦𝐚𝐫𝐥𝐲:Apk Download 

Yana matuƙar amfani saboda yana gyaran (𝘀𝗽𝗲𝗹𝗹𝗶𝗻𝗴 𝗮𝗻𝗱 𝗴𝗿𝗮𝗺𝗺𝗮𝗿 𝗰𝗵𝗲𝗰𝗸𝗶𝗻𝗴). Sannan ya bada dama domin scanning na rubutu don gano ƙwafarsa akayi ko mallakin wani ne daban.

𝟖. 𝐂𝐡𝐚𝐭𝐆𝐏𝐓: Apk 

Tana ƙarfi sosai, kuma taimakawa wajen ƙirƙirar rubutu, kawai zaka bata umarnin abinda zata fidda maka, sannan tana taimaka wajen gyaran (𝘀𝗽𝗲𝗹𝗹𝗶𝗻𝗴 𝗮𝗻𝗱 𝗴𝗿𝗮𝗺𝗺𝗮𝗿 𝗰𝗵𝗲𝗰𝗸𝗶𝗻𝗴). Amma mutane dayawa na amfani da ita sosai, dole sai ka koyi yanda zaka bata umarni ta fidda maka rubutu wanda ya fita daban dana kowa.

𝟗. 𝐏𝐡𝐨𝐭𝐨𝐑𝐨𝐨𝐦:Apk Download 

Ana amfani da wannan application wajen cirewa hoto background da haɗa profile pictures da dai sauransu, yanzu zaka iya amfani dashi wajen cirewa hotunan ka background. Baka buƙatar Photoshop ko Coreldraw.

𝟏𝟎. 𝐆𝐨𝐨𝐠𝐥𝐞 𝐃𝐫𝐢𝐯𝐞:Apk Download 

Zaka iya amfani da wannan application wajen ajiye kayayyakin tarihi, kona kasuwanci, da kuma files kamar videos, musics, PDF, da dai sauransu. Yana da cloud space da ya kai girman 𝟭𝟱𝗚𝗕 𝗠𝗲𝗺𝗼𝗿𝘆 wanda zaka iya ajiye abubuwan ka acikin sa, kyauta ne ga kowa.

Post by Alamin Haruna Rashid

Download free APK files and Android apps from APK Store. Explore safe, verified, and updated Android applications across multiple categories...

Post a Comment