Stay connected with us Apkstore for Get Latest Update Now. apkstore.com.ng

Crypto Market Sentiment Analysis !!!  


 Crypto Market Sentiment!!  

A lokuta da dama Zakaji ana maganar "SENTIMENT", kuma ana faɗar shi da kalmomi daban-daban.


Misali:

1. Market sentiment.

2. News/Event Sentiment!.

3. SOCIAL MEDIA SENTIMENT.

4. INVESTORS SENTIMENT!.


Da suaransu.

A yau insha'Allah zanyi bayanin Ma'anar SENTIMENT ta yadda da zarar kaji an Ambaci "SENTIMENT" zaka fahimta!!

Let's start 

Menene ma'anar Sentiment a kasuwar Crypto: Sentiment Yana nufin Ra'ayi/Hali da mutane suke ciki a kasuwa. Wanda wannan Ra'ayin na mutane akan kasuwa yana taka muhimmiyar Rawa wajan TASHI (BULLISH) ko sauka(BEARISH) na kasuwa. 

 SENTIMENT shine Ma'aunin da Muke Amfani dashi wajan gano me kasuwa/Project zai yi A gaba!.

Akwai Abubuwa(Tools) Da muke Amfani dasu wajan gano/fahimtar wannan SENTIMENT ɗin.

Waɗannan Abubuwan sune kamar haka:

1. FEAR and GREED Index.

2. News And Events.

3. SOCIAL MEDIA.


1. FEAR and GREED Inde: Shine "The Most popular Tool" (Ma'auni mafi ƙarfi da sauƙi) da muke Amfani dashi a kasuwa wajan Measuring Sentiment. 

A kasuwar Crypto mutane suna shiga yana yi 4. Kuma duka muna iya gane wa ta hanyar Amfani dashi wannan "FEAR and GREED" Index ɗin.


Yanayi 4 da mutane suke shiga sune kamar haka:

1. FEAR (TSORO).

2. GREED (HAƊAMA).

3. EXTREME FEAR (Tsananin Tsoro).

4. EXTREME GREED (Tsananin haɗama).


Wannan Ma'aunin Da Muke kalla wajan fitar da SENTIMENT Yana juyawa ne tsakanin 0 zuwa 100:


Yadda yake aiki shine:

From 0-25 = Extreme Fear: Hakan yana nuni da cewa kowa yana cikin "Matsanancin Tsoro" a kasuwar crypto.


From 26 - 49 = FEAR: Hakan yana nuni da cewa Al'umma suna cikin "Tsoro".


From 50-59 = NEUTRAL: Hakan yana nuni cewa kasuwa tana tsaka tsaki, Al'umma basa cikin tsoro, kuma basa cikin haɗama.


From 60 - 70 = GREED: Hakan yana nuni da cewa Al'umma sun fara shiga haɗama.


From 71-100 = EXTREME GREED: Hakan yana nuni da cewa An shiga matsananciyar Haɗama! Kowa zuwa yake ya siya kawai A wannan yanayin ne wanda bai san yadda ake siya ko SIYAR da crypto Bama, yake ɗauko kuɗin shi yace a siya masa.


Hanya mafi sauƙi da zaka bi wajan Amfani da wannan "INDEX" ɗin shine:

 Kayi Amfani da strategy da "WARREN BUFFETT" yake Amfani dashi:


1. Buy when people a FEARFUL (Ka siya lokacin da mutane suke cikin Tsoro).


2. SELL when people are GREEDY (Ka siyar lokacin da mutane suke cikin Haɗama).


Simple 😄.


Wannan shine Strategy da Manya Manyan Analyst na duniya suke Amfani dashi a bangaren Sentiment. Duk lokacin da kuka kasan ce a cikin Tsoro, su A lokacin suke shiga kasuwa, lokacin kuma da kuka kasan ce a Farin ciki(Haɗama) lokacin suke fita daga kasuwa!.


Mutanen nan basa son ganin ɗan baiwa yana farin ciki fah😂.


Zaku iya Nemo wannan INDEX ɗin a cikin wannan channel ɗin👉: 

Channel join 

Ko kuma ku dinga duba Story na, na Facebook ina ɗorawa kullum.

Fatan wannan bangaren ya fita!?


Bari mu cigaba.


NEWS And EVENTS Sentiment: A wannan bangaren muna kallon News(Labaran kasuwa) Da kuma Events(Wasu Abubuwa da ake ƙoƙarin gudanar wa a cikin kasuwa).


A ɓangaren "NEWS" Labarai, Akwai wanda suka shafi kasuwa gaba ɗaya, akwai kuma wanda suka shafi wani bangare na kasuwa(Ma'ana wani Project/Ecosystem dake ƙarƙashin Crypto).


Misali:

NEWS SENTIMENT: wanda ya shafi kasuwar crypto gaba ɗaya sune:

"SEC Chair Gary Gensler says Bitcoin is not a security."


"BREAKING: Binance Founder CZ released from prison."


" Donald Trump uses Bitcoin to pay at a bar in New York."


Duka waɗannan Labarai ne da suka shafi gaba ɗaya kasuwar Crypto. Wanda zasu zamar maka ma'auni da zaka iya Amfani dashi wajan fahimtar kasuwa is BULLISH ko BEARISH.


A ɓangaren "EVENT SENTIMENT" kuma wanda suka shafi kasuwar crypto gaba ɗaya sune kamar haka:


"Michael Saylor's MicroStrategy raises $1 billion to purchase more Bitcoin"


"Hong Kong set to approve spot Bitcoin & Ethereum ETFs by Monday, Bloomberg reports."


Ko kuma Kamar misalin Film da akace za'a saki kwanan nan, wanda zai tona Asirin Ainihin waye SATOSHI NAKAMOTO.(Wanda wannan Film ɗin bashi da wani tasiri akan farashin Bitcoin☺️, kawai dai za'a yaɗa FUD ne a cikin Al'umma).

Duka waɗannan Abubuwa ne da aka shirya za'ayi nan gaba a kasuwa, kuma zuwan su zai iya zama (BULLISH) ko (BEARISH), a kasuwa.

Kaga kenan zamu kira wannan EVENT ɗin sentiment Wanda zamu gano farashin kasuwa a nan gaba!!

 

Fatan An fahimci wannan bangaren shima da kyau!?.

Bari mu cigaba.

To idan zamu kalli SENTIMENT daya shafi wani bangare na CRYPTO industry kuma fah?


Misali:

SENTIMENT analysis akan $DOGS.

SENTIMENT analysis akan $SHIB.

SENTIMENT analysis akan $HAMSTER .  da sauran su.


Duka waɗannan muna mayar da hankalin mu ne sosai wajan "SOCIAL MEDIA SENTIMENT"(Ma'ana abun da mutane suke faɗa akan Token ɗin a TWITTER ko Facebook. Domin kuwa duk wani Hype da akeyi akan irin wannan Tokens ɗin ana yin shine a cikin social media.

 Ra'ayin mutane da Abun da suke faɗa akan su yana tasiri matuƙa akan Tashi (BULLISH ko saukar (BEARISH) su.

MISALI:

NEWS SENTIMENT Akan DONGs:

1. DOGs TVL ya tashi da kaso 50% a 24hours da suka wuce.


NEWS SENTIMENT Akan HAMSTER:

2. "Whales suna tsoron Siyan Hamster saboda Supply ɗinshi, yayi yawa!.


Da sauran misalai dai. wanda nasan kun fahimta.

 Duk wani Abu da zai taɓa kimar wannan project ɗin ko kuma zai ƙara masa daraja yana da matuƙar tasiri wajan tashi(BULLISH, ko sauka (BEARISH) na wannan Token ɗin.

Sannan Akwai kuma wasu projects ɗin da idan har wani Abu ya shafe su yana shafar Gaba ɗaya kasuwar ne:

Kamar misali: 

BITCOIN (BTC): Duk wani Abu da ya shafi Bitcoin Yana shafar kasuwa gaba ɗaya. Saboda Bitcoin yayi Dominating 56% Na gaba ɗaya Total crypto market capitalization.


2. ETHEREUM ya kwashi 13% na Total market capitalization, Sannan kuma akwai manya manyan project da suke a ƙarƙashin shi. Kaga kuwa duk abun da ya shafe shi yana shafar sauran Token a kasuwa!

3.USDT.

4. BNB. 


Duka irin waɗnnan Projects ɗin suna da Influence sosai a cikin kasuwa, ta yadda idan wani Abu ya shafe su, yana iya shafar Gaba ɗaya kasuwa!!.


Da fatan bayanin ya fita sosai!.

Idan ka ƙaru, kayi sharing Domin wasu ma su Amfana!

Download free APK files and Android apps from APK Store. Explore safe, verified, and updated Android applications across multiple categories...

Post a Comment