ISTIGHFARI
MENENE ISTIGHFARI ?
Yana nufin neman gafara da afuwar Allah da yafiyarsa ga abinda ya gabata na sabon Allah bayan tuba,da kuma neman yafiyarsa ga abinda kayi na laifi cikin abinda kasani da wanda baka sani ba,tare da neman afuwar Allah cikin abun da ka kasa na bin umarnin Allah da ibada.
1.ISTIGHFARI : Allah ya bamu labarin abinda Annabi Nuhu (as) yake gaya ma Mutanensa. Yace:
"NACE (MUSU) KU NEMI GAFARAR UBANGIJINKU DOMIN SHI MAI GAFARA NE. ZAI SAUKAR MUKU DA RUWA DAGA SAMA, KUMA YA QAREKU DA DUKIYA DA 'YA'YA, KUMA ZAI SANYA MUKU GONAKI KUMA ZAI SANYA MUKU QORAMU (Wato albarkacin Istighfarin nan Allah zai gafarta zunubanku, kuma zai yalwata arzikinku ta fuskar 'ya'ya da dukiya da gonakai da Qoramu da kuma ruwan sama mai albarka.
Manzon Allah (saww) yace duk wanda ya yawaita Istighfari Allah zai yaye masa damuwarsa kuma zai azurtashi ta inda ba ya tsammani.
Daga cikin hanyar da Allah yake kawowa bayinsa arziki mai yawa anan duniya da lahira bayan Imani da jin tsoron Allah babbar hanyar itace:
ISTIGHFARI DA TUBA
Yana nufin neman gafara da afuwar Allah da yafiyarsa ga abinda ya gabata na sabon Allah bayan tuba,da kuma neman yafiyarsa ga abinda kayi na laifi cikin abinda kasani da wanda baka sani ba,tare da neman afuwar Allah cikin abun da ka kasa na bin umarnin Allah da ibada.
Manzon Allah ﷺ yana cewa:-
*(Dukkan wanda ya yawaita Istighfari ,Allah zai sanya masa mafita daga cikin dukkan kunci da yake ciki,kuma ya fitar da shi daga cikin dukkan wata Damuwa,kuma ya azurta shi daga inda baya tsammani)*.
@ ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﺔ ﻓﻰ ﺳﻨﻨﻪ
ﺑﻦ ﻛﺜﻴﺮ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :
Yana cewa:-
Dukkan wanda ya siffantu da siffar yawaita Istighfari,Allah sai azurta shi da:-
1.Allah ya saukaka masa samun arzkiqi kuma ya yawaiwata Arziqinsa.
2.Kuma Allah ya sanya masu sauki acikin dukkan al'amarunsa.
3.Kuma Allah zai bashi kariya aciki n lamarinsa,kuma ya karfafe shi acikinsa.
@ ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢ ( 450 /2 )
ﺇﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ) :
Yana cewa:-
Wani lokaci na kan sami kunci cikin wadansu al'amurana sai na dauwama yin ISTIGHFARI,na kanyi Istighfari a kalla sau dubu sai na sami budin Allah a cikin al'amaruna.
ﻗﺘﺎﺩﺓ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :
Yana cewa:-
Lallai wannan Alqur'ani yana shiryar da yi maku nuni zuwa ga cutukanku da maganin cutukanku,amma cutukanku shine SABON ALLAH DA ZUNUBI,maganin cutukar kuwa shine:ISTIGHFARI_*.
ﺷﻌﺐ ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ ﻟﻠﺒﻴﻬﻘﻲ ( 6883 )
ﺍﺑﻦ ﺍﻟﻘﻴﻢ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :
Yana cewa:-
Yawan sabo da zunubi yana janyo damuwa da tsoro da kuncin rayuwa,da cutukan zuciya,kuma babu wani magani ga wannan cutukan sai ta hanyar TUBA da ISTIGHFARI.
KARIN WASU HANYOYIN DA SUKE JANYO BUDEWA KOFOFIN ARZIKI
2.TSAIWAR DARE (Qiyamul Layl) : Manzon Allah (saww) ya nuna mana Muhimmancin Tsaiwar dare ya ce tana janyo ma mutum samun girman matsayi awajen Allah. Kuma duk wanda ya hana idonsa barci cikin dare don neman yardar Allah, Shi kuma Allah zai faranta zuciyarsa da rana.
2. SADAQAH : Sadaqah itama babbar hanyar budewar kofofin Arziki ne. Domin kuwa Allah yana cewa :
"IDAN KUKA BAMA ALLAH RANCHE, RANCHE MAI KYAWU, TO ZAI NINNINKASHI GAREKU KUMA ZAO GAFARTA MUKU.. ".
Kuma yace "DUK ABINDA KUKA CIYAR NA WANI ABU, TO (ALLAH) SHI ZAI NINKASHI KUMA SHINE MAFI ALKHAIRIN MASU AZURTAWA".
3. ZIKIRIN ALLAH : Zikirin Allah, Karatun Alqur'ani da Salatin Manzon Rahama (saww) su ke Sanya zuciya ta samu nutsuwa azahiri da badini. Kuma ta hanyar zikirin Allah mutum yana samun yayewar Talauci da Qunci. Kuma yana samun kusanci da Allah da jibintar lamarinsa aduniya da lahira.
Allah yasa mu dace da samun wadannan falaloli. Allah ya yaye mana Quncin rayuwa, ya Qara rufa asiranmu aduniya da lahira Ameeen.