Assalamu Alaikum Warahamatullah! Yan’uwa Barka War Haka.
dafarko Zance Duk Lamarinda zaka gina to ka ginashi akan turba ta Gaskiya.
Domin ita Soyayya Gaskiya Ce, Amma marasa Gaskiya kan shigeta har su batata koma su tozartata nayi nazari akan wasu kalamai na soyayya.
SHIN KASAN KALAMAN SOYAYYA 25 DA MAZA BASU GAJIYA DA GAYAWA WAJEN MATAN SU.
Na ci karo da wannan makalar a cikin wasu
bincike-binciken da nake gudanarwa kan halayen mata, shi ne na ga yana da kyau membobinmu a wannan Shafin namu musamman maza su fahimci wasu daga cikin halayen.
Daga bisani, mu Tattaro ra’ayoyin sauran jama’a, makaranta wannan shafin mai farin jini.
A binciken nawa, na fahimci babbar matsalar da maza ke fuskanta a kan zama da mata a yau shi ne rashin fahimtar yarensu. Ma’ana Lugga ko salon da zantukansu da inda maganarsu ke fuskanta.
Amma kafin nan, ba ri mu yi tsakaci
kan mace da yadda take gudanar da harkokinta a zahirance.
Masana harkokin mata, sun tafi a kan cewa
mace ta fi aiki da zuciya fiye da kwakwalwa,
sabanin namiji da ke aiki da tsantsar
kwakwalwarsa, gami da hikimar da Allah Ya
huremasa. Bisa wannan dalilin ne idan
mutum ya aikata wani abu, a ce da shi, ‘Habawane…! Me ya sa kake abu kamar mace?’
Nesaba kusa ba, namiji ya dara mace zurfin tunani da nazari bisa wannan dalilin. Hakan kuwa ya samo tushe ne daga cikin littafin Allah mai tsarki, wato Alkur’ani; inda Allah (SWT) da kanSa Ya zayyano martabobin namiji fiye da mace, sannan
bayyana dalla-dalla fifikon namijin bisa mace,
kamar yadda malamai suka karantar da mu.
Amma ina son masu karatu su gane cewa, zan takaita wannan tattaunawar a kan matanmu na wannan zamanin. Domin kada wani ya tashi da husumarsa ya ce, ina kokarin muzanta mata a Musulunci.
Sanin kanmu ne cewa akwai manyan bayin Allah (mata), wadanda Allah Ya zaba a cikin addinin Musulunci, wadanda kuma suka taka
muhimmiyar rawar ganin Musulunci ya tabbata.
Su zababbu ne na Allah, su iyaye ne abin
alfahari gare mu, sun kasance fitilu a gare mu.
To, wannan makalar tana kallon rayuwarmu
matanmu ne na yanzu Da fatan an fahimta.
Me ya sa aurarrakinmu na zamanin nan ba sayin karko?
Me kuma ya sa maza suka kasafahimtar abokan zamansu?
Bisa wani dalili yasa mata ba su da kunyar kallon namiji, sannan za su iya furta masa kowace irin kalma da ta zobakinsu!
Ina alkunyar da aka fi sanin mace da ita?
Me ya sa aka watsar da kyawawan al’adu,
wadanda suke zame wa mutane abin koyi?
Kafin mu amsa wadannan tambayoyin, yana da kyau mu kalli wasu zantukan da na binciko, a wani nazarin musamman da na gudanar da halayen mata kamar yadda na fadi a sama, ko maza za su iya daukar darasi a kai?
Ga su nan kamar haka:
Zamu dora inda muka tsaya sa....