Stay connected with us Apkstore for Get Latest Update Now. apkstore.com.ng

KALAMAN SOYAYYA MASU KWANTAR DA HANKALI


KALAMAN SOYAYYA MASU KWANTAR DA HANKALI

Sonkine Sila Kuma Majinginar Kalaman Ruhu Mai Isar Da Muhimmin Sako Wanda Ya Kunshi So Zallah Tare Da Tasirin Zama Cikin Inuwar Shaukin Annashuwar Zuciyata

♥️♥️♥️♥️.


Hankali Abun Tattalin Rayuwar Amincin Soyayya Nidake Mun Kasantu Cikin Wata Duniya Ta Musamman Wadda Ta Qawatu Da Wasu Furanni Na Musamman Akan Yanayin Tafiyar Masoya Zuwa Babban Birnin Masoyan Asali ♥️♥️♥️♥️.


Dake Na Kuduri Aniya Da Niyyar Alakantuwa Ta Musamman Wadda Cikin Yanayin Yanda Nake Tafiyar Da Soyayya Ta Agareki Shine Shaidar Lallai Ina Miki Soyayyar Da Batada Karshe ♥️♥️♥️♥️.


Inaso In San Adadin Abinda Ranki Yake Matukar So Nikuma Zan Sadaukar Miki Da Dukkan Farin Cikina Domin Yakara Inganta Lafiyar Murmushin Dake Fitowa Daga Fuskarki ♥️♥️♥️♥️.


Budewar Ido Akowace Safiya Murmushin Farko Dake Fitowa Daga Bakina Bakomai Bane Face Shaukin Sonki Wanda Ke Mafarkar Da Zuciyata Da Yawan Begenki

♥️♥️♥️♥️.


Acikin Jerin Zababbun Mata Masu Kyau Kin Ciri Tutar Zama Sarauniya Mai Isar Mulkin Kasaitar Dake Kara Kusanto Da Shaukin Dumbin Sarakai Masu Takama Da Mulkin Sarautar Kyawawa ♥️♥️♥️♥️.


Akan Iyakar So Mabudin Kofar Shiga Cikin Fadar Sarauniyar Zuciyata Cikin Yanayin Sabon Shigar Abinda Ake Kira Sonki Nidai Kawai Ina Begenki

♥️♥️♥️♥️


Matukar Inaso Toh Daga Can Cikin Zuciyata Nake So Shiyasa A Kullum Nakeso In Kara Jaddada Miki Kalmar So Tunda Rayuwata Gabaki Daya Ke Take So

♥️♥️♥️♥️


Sani ahalusunnah ❤️karkuga laifinafa😎Cikin Salo Irin Na So Nakeson In Isar Da Sakon So Zuwaga Wadda Nakeso Inason Samun Abunso In Sakashi Cikin Sakon So Domin Yabani Kalmomin Da Nakeso Wajen  Faranta Ran Wadda Nake So


Ilimin Fahimtar Sakonnin Zuciyarki Sune Silar Dake Sa Ina Gane Abunda Kikeso Daga Lokacinda Idona Yakalli

 Kyakkyawar Suffarki.


Matsakaiciyar Alamace Wadda Ta Nuna Girma Da Kwarjinin Abinda Na Mallaka A Zahiri Wajen Ganin Nasamu Nutsuwa Idan Ina Tare Dake Yantuwar Kai Daga Kunci Kece Silar Yayewar Damuwata Hakika Dolene Zuciyata Tayi Miki Son Da Bashida Karshe Sauyin Yanayin Zamani Bazai Iya Sauya Fasalin Tsarin Sonki Wanda Yakafa Sansani Acikin Raina Ba.


Bazan Kaucewa Soyayyarki Ba Saidai Gyara Zama Cikin Abinda Yashafi Tsantsar Kaunarki Wadda Nakeyi Babu Dare Babu Rana


Kullum Burin Raina Tayaya Zan Samu Ganinki Ya Mai Saurin Fahimtar Yaren Zuciyata.



               ♥♥FARILLAN SOYAYYA♥♥ 

1 Tsoron Allah.♥

2 Hakuri.♥

3 Rikon Amana.♥

4 Kulawa.♥

5 Rikon Alkawari.♥

6 Fadar Gaskiya.♥

7 Tsafta.♥

8 Kwalliya.♥

9 Kalaman Soyayya.♥

10 Kunya.♥

11 Kishi.♥

12 Kulawa.♥

13 Iya magana.♥


          ♥♥SUNNONIN SOYAYYA♥♥ 


1 Zuwa zance.♥

2 Kyauta.♥

3 Tattali.♥

4 Yabawa.♥

5 Tarairaya.♥

6 Kawar da kai.♥

7 Mutunta juna.♥


 ♥♥MUSTAHABBAN SOYAYYA♥♥   

1 Shagwa6a.♥

2 Iya kallon SO.♥

3 Dawainiya.♥

4 Mutunta dangin juna.♥

5 Iya tura sako a waya.♥

6 Kiran juna a waya.♥

 7 Yiwajuna Murmushin Soyayya.♥


              ♥♥ALAMOMIN SO♥♥


Akwai alamomin dake fitar da so, masu

tarin yawa suke bayyana soyayya ga kadan

daga ciki.

          1. ♥KUNYA

da zarar soyayya ta fara shiga ko da ba a yi furuci ba sai kunya ta shiga tsakani, sai aga masoyan a junansu suna jin kunyar juna. 

                2. ♥YAWAN KALLO


wannan alamace ta soyayya,misali ta hanyar yawan satar kallo, idan masoyi yana kallon a bin son shi da ya waiga sun hada ido xai kawar da kansa. 

                3. ♥FADUWAR GABA

a lokacin da soyayya ta fara shiga xuciyar  saurayi ko budurwa xa ka samu da zarar sun hango juna kowa sai gabansa ya fadi .

               4. ♥YAWAN AMBATO

matukar soyayyar saurayi ta kafu a zutciyar budurwa ko ta budurwa ta shiga ran saurayi xaka samu yana yawan kawo labarin wanda yake so din ako yaushe, kuma duk inda ya ji an fara labarin wanda yake son xa kaga ya nutsu yana sauraro. 

                       5. ♥TAUSAYI♥ 

soyayya musamman ta gaskiya tana tare datausayi  Kuma sau tari zakaga masoyi ko masoyiya suna matukar tausayi ga junansu har hakan na haifar da damuwa ko saurin kuka musamman mata. 


Assalamu Alaikum. Barka da hawa online!!!

Akwai dadin karantawa sosai. 

Nabarku lafiya daga naku aminu umar aminu SOYAYYAR GASKIYA NAKEMIKI.

Post by  Msz...

Download free APK files and Android apps from APK Store. Explore safe, verified, and updated Android applications across multiple categories...

إرسال تعليق