MARKET CAPITALIZATION
Marketcap na nufin adadin jari ko kuɗin da yake cikin cryptocurrency, ana lissafa yawan Marketcap ne ta hanyar daukar farashin da coin yake dashi, sai a ninka shi da yawan adadin coin (Circulation Supply) ɗin da yake hannun mutane.
( Price × Circulation Supply )
Akasari idan kaga Marketcap na coin yana da girma, toh hakan na nuna maka wannan coin ya dade a kasuwa ko kuma an sanshi sosai. Amma fa hakan ba ma'auni ne dake nuna shine yafi kamata kayi Investing a ciki ba.
Akwai rabe-raben Marketcap guda uku a kasuwar cryptocurrency:
1. High Marketcap: Shine coin ɗin da Marketcap nasa ya fara daga Biliyan ɗaya zuwa sama, su irin waɗannan coin ɗin suna da Risk Security idan ka siye su. Amma basu cika opportunity mai girma ba.
2. Average Marketcap: Irin coin ɗin da suke da Marketcap daga 200Million zuwa irin 800Million su ake kira da Average M.C, suna da Risk Security amma basu kai na farko ba. Risk ɗinsu shine asari coins da suke wannan matakin, kodai suyi gaba ne ko su faɗi.
3. Low Marketcap: Coins masu Marketcap daga 500k zuwa irin 150Millions duk ana iya saka su anan, suna da Risk sosai da sosai. Amma kuma da yawan irin waɗannan coins din sunfi opportunity, nan da nan zasu ninka maka kuɗaɗen ka ninki ba ninki.
"Lissafin High, Average da Low M.C ya danganta ne da adadin kudin da a lokacin yake kasuwa gabaki daya, idan jarin kasuwar yayi yawa ko yayi kadan yana chanzawa"
Ƙarin Bayani; Duk coin din daka ga ya tashi a kasuwar crypto toh sai Marketcap nasa ya ƙaru, yanzu misali coin ɗin da yake farashin $0.5 dole sai M.C ɗinsa ya ninka yawan sa sannan zai kai $1.
Mu dauka Marketcap ɗin yana $1Million, toh sai ya dawo 2Million sannan zai kai $1 nan. Shiyasa ƙananan coins da suke da ƙaramin M.C sunfi yiwuwar su ninka kuɗin su fiye da masu babban M.C.
Apkstore......hausa ........Tech..........