Stay connected with us Apkstore for Get Latest Update Now. apkstore.com.ng

SHIN KI KASANCE MACE MAI KUNYA KO KUMA A KASIN HAKA? 



    SHIN KI KASANCE MACE MAI KUNYA KO KUMA A KASIN HAKA?   

                                           Kunya A don yar Macce       

Mace da kunya aka santa domin kunya ado ne kuma yana kara kawata mace,ana son mace mai kunya a ko ta ina mace mai kunya abar birgewa ce.

Amma da yawa a yanzu mata anyi watsi da kunya,an daina jin kunya ana bin cewa wai wayewa ce ko kuma dai menene,to kisani cewa kunya abu ce mai kyau ga rayuwar ki.

" Muna yawan fuskantar matsalolin rayuwane tun lokacin da KUNYA !!! Tayi k'aranci a tsakaninmu, mun mance cewa kunya wata d'abi'a ce daga cikin dabi'un musulunci wanda ake kwadaitar da musulmi na gari ya siffantu da ita.

Yayinda ba'a damu da MATSAYIN KUNYA A MUSULUNCI BA an mance kunya a addinin musulunci d'abi'ace dake sanya mutum aikata kyawawan ayyuka ababan so ga ma'abocin ta, ta kuma hana shi aikata munanan ayyuka.


 Manzon ALLAH ( S.A.W) yace"

"KUNYA wani rassa ko yanki ne daga cikin imani." [sahihun nasa'i 5020].


 Manzon ALLAH ( S.A.W) ya kuma cewa.

"KUNYA bata zuwa da komai sai alhairi."

a wani wajen kuma yace: "kunya dukkanta alkhairi ce." Sahihaini.


 Manzon ALLAH yace. " Lallai ALLAH  mai yawan kunyane kuma mai son suturtawa ne, yana son suturtawa da kunya." [ Abu-dawud da nasa'i]


Manzon ALLAH yana kuma cewa.

"Yana daga abunda mutane suka riska daga cikin kalaman Annabawan farko, idan baka jin kunya to ka aikata abunda kaga dama." ( Bukhari).


A wani wurin kuma Manzon ALLAH  yace.

"lallai kowanne addini yana da wani hali mai kyau,halin Musulunci shine kunya."

(Muwadda Malik da sunan ibn majah)


 Ibn sa'adiy ( Rahimahullah) yana cewa.

" Da kunya ake samun rayuwar imani,wato imani yana rayuwa ne idan akwai kunya acikinsa, da kunya ne bawa yake barin dukkan abunda zai janyo masa zubar da mutumci da matsayi,da kunya ne aka tabbatar da dukkan halayen masu kyau,domin kunya itace tushen dukkan hali mai kyau abun yabo,kuma ita ke korar da dukkan hali mummuna abun zargi."

( Attaudihu wal bayan:95)

 "Ibn Uthymeen (Rahimahullah) yace:

" Kunya wani sifface ko dabi'ace da take sanya mutum ya aikata dukkan abunda zai sanya masa yabo da dauk..

Allah ya datar damu duniya da lahira Ka samu cikin sahun masu Jin kunya ....

Download free APK files and Android apps from APK Store. Explore safe, verified, and updated Android applications across multiple categories...

Post a Comment