Stay connected with us Apkstore for Get Latest Update Now. apkstore.com.ng

SIFFOFIN NAMIJIN DA ZA' A AURA DOMIN TSIRA DUNIYA DA LAHIRA....

 

   

                              💠SIFFOFIN NAMIJIN DA ZA A AURA💠

👉 Ya zama mai addini, mai kiyaye dokokin Allah, ko da kuwa ba malami ba ne, lallai mai addini shi ne ake tsammanin kiyaye hakkokin auratayya daga gare shi.

👉 Ya kasance ya dan haddace wadansu Ayoyin Alqur'ani, domin suna karawa bawa Imani, wanda ya haddace ayoyi kuma yana kiyaye dokokinsu babban mutum ne a wurin Allah.

👉 Ya zama mai tausayin mata, ba mai duka, tsangwama, zagi, takura da cin mutunci ba, a inda babu gaira babu dalili.

👉 Ya kasance yana da kuzarin biyan bukatan Iyalinsa, nemo mata abinci, sutura, kayan kwalliya, wurin zama da abubuwan masarufi na yau da kullum. Annabi (ﷺ ) yace: "WANDA YAKE DA HALI DAGA CIKINKU YA YI AURE..." [Bukhaqi 5065, Muslim1400].

👉 Wanda ganinsa zai faranta ran matarsa, sannan da zamantakewa mai kyau.

👉 Ya kasance ana tsammanin samun zuriya daga gare shi, akan gane hakanne ta hanyar 'yan uwansa ko zuriyar sa. 

Koda yake haihuwa kyautar Allah ne, yakan bayar da shi ga wanda yaga dama, wani kuma ya sanya shi AƘIIM, kamar yadda yace: "YA KAN SANYA WANDA YA GA DAMA AƘIIM (wanda ba ya haihuwa)" [Shura:50].

👉 Kuma ya kasance ya dace da matar, ta wajen hali, matsayi da fahimtan juna, da wannan ake sa ran samun zaman lafiya a tsakani.

Jan kunne ga ƴan uwa mata kada abin duniya ya sa ku kuskura ku auri mutumin banza, mai halin mutanen iska, domin za ku shiga mayuwacin halin wanda hakan zai sa baza ku ji daɗin rayuwa ba har abada.

Sai Mu Hadu A darasi na gaba insha Allah.

Allah ya sa mu dace ya bamu abokan zama nagari.

Download free APK files and Android apps from APK Store. Explore safe, verified, and updated Android applications across multiple categories...

Post a Comment