Stay connected with us Apkstore for Get Latest Update Now. apkstore.com.ng

Tarihin Bermuda Triangle: Me Za Ka iya Sani Game da Bermuda Triangle (Tsibirin Shaidan)?



Me Za Ka iya Sani Game da Bermuda Triangle (Tsibirin Shaidan)?

Bermuda Triangle

Shekaru da dama tun daga yammacin turai, America, Africa da sauran sassan duniya wannan suna na Tsibirin Shaidan ya jima a bakunan mutane, kuma ba wai don gargajiya kawai ba, a'a sai dai don wani abun al'ajabi da ya sha faruwa a wancen lokaci. 


Bermuda Triangle wanda aka fi sani da Tsibirin Shaidan a gargajiyance wani tsibiri ne a kusa da kasar Mexico tsakanin Bermuda, Miami da Puerto Rico, inda wani teku ya kasance mai matukar abun al'ajabi da yake hadiye jiragen sama idan sun zo giftawa ta samansa. 


Jirage da dama sun jima suna bata a wannan yankin ba tare da sanin dalili ba, ba sai daga bisani aka gano cewa akwai wani abun da yake da alhakin lakume wadannan jiragen. 


A lokacin ne mutane suka tsorata da lamarin suka yi wa wajen lakabi da Devil's Triangle wato Tsibirin Shaidan. Daga nan ne masana suka dukufa wajen binciken kwakwaf kan gano ainihin abun da yake farywa; shin wata halitta ce wacce ba a san ta ba a wajen, shaidanu ne ko kuma mene ne. 


Bayan an gudanar da bincike na tsawon shekaru wanda fitattun masana kimiyya suka gudanar, sai aka gano cewa ba wata halitta ba ce a cikin wannan teku da take lakume wadannan jirage, ba kuma shaidanu ba ne suka kafa daula a wurin, binciken ya tabbatar da cewa kawai tsananin karfin maganadison tekun (excessive force of gravity) ne kawai ya ke jango duk abun da ya je ketawa da samansa. 


Bayan wasu lokuta aka kara tabbatar cewa hakika wannan bincike bai ci karo da duk wasu ingantattun nazariyyoyin kimiyya ba, sai dai kara tabbatar da su yayi kamar nazariyyar Albert Einstein ta Theory of Relativity da kuma ta Sir Isaac Newton ta Theory of Gravitation. 


Hakika wannan bincike ya tabbatar da cewa tsananin karfin maganadison da ke tekun ne yake jango duk wani abun da ya so giftawa da samansa don haka wadannan jiragen suke salwanta. Har ila yau, binciken ya kara gano wadannan jiragen da suka nutse a karkashin tekun shekaru aru-aru baya.


Wannan bincike ya kara tabbatar da kasantuwar blackhole da danginsa.


Post by —Mohiddeen Ahmad 



Download free APK files and Android apps from APK Store. Explore safe, verified, and updated Android applications across multiple categories...

إرسال تعليق