SHEIKH MAHMOUD KHALIL AL-HUSARI
ٱلشِـيـْخ محمُود خَلِيـْل الْحُصـري
- HAIWUWA: A garin Tanta Egypt
- SHEKARA/H : September 17, 1917
- S/ YA RASU : November 24, 1980 {age 63}
- farkon wanda ya fara yin kaset cikakke na Alkur'ani a duniya,da riwayar Imamu Hafsu daga Imamu Asim a shekarar 1961.
farkon wanda ya fara yin kaset cikakke na Alkur'ani a DUNIYA, da riwayar Imamu warshu daga Imamu Nafiu a 1964.
- farkon wanda ya fara yin kaset cikakke na Alkur'ani a duniya, da riwayar Imamu Qalun daga Imamu Nafiu a 1968.
- farkon wanda ya fara yin kaset cikakke na Alkur'ani a duniya, da riwayar Imamud Dury daga Imamu Abu Amru dan Ala A Shekarar 1968.
- farkon wanda ya fara yin kaset cikakke na Alkur'ani a duniya mai dauke da salon koyar da Alkur'ani (Mu'allim) 1969.
- farkon wanda ya fara yin kaset cikakke na Alkur'ani a duniya da salo na tafsiri 1975.
- farkon wanda ya fara yin karatun Alkur'ani a zauren majalisar dinkin duniya 1977.
- Farkon wanda ya fara yin karatun Alkur'ani a fadar sarauniyar Ingila 1978.
- Farkon wanda ya fara karanta Alkur'ani a fadar white house da majalisar dattawa ta Amurka (congress).
- shugaban makaranta Alkur'ani na duniya a zamaninsa.
- Yayi wasiyya da sulusin dukiyarshi domin hidimtawa Alkur'ani mai girma da makaranta Alkur'ani.
- Mai son kwarewa a fannin karatun Alkur'ani ya makalkale mishi, babu kari babu ragi.
Mutuwar sa....
Sheikh Al-Husari rasuwa a yammacin ranar Litinin 16 ga Muharram 1401 Hijira daidai da 24 ga watan Nuwamba 1980 bayan sallar isha'i, ya dawo daga aikin Hajji, ya karanta Alkur'ani mai dadi da muryarsa ta karshe a masallatai biyu masu alfarma.
Sousce: echoroukonline.com
Allah jikansa ya gafarta masa tare da sauran hadiman Alkur'ani
mai girma, Ameen.
Posted by Apkstore.