Stay connected with us Apkstore for Get Latest Update Now. apkstore.com.ng

TECHNICAL ANALYSIS CANDLESTICK :TWEEZER CANDLESTICK PATTERNS 


TECHNICAL ANALYSIS CANDLESTICK PETTERNS 

 TWEEZER CANDLESTICK PATTERNS 

Tweezer pattern tagwayen candles da ke bayyana a matsayin alamar da ke nuni da canjawar tafiyar Price. Suna bayyana ne a saman tafiyar price (uptrend) ko kuma a qasan tafiyar price (downtrend). Idan sun bayyana a saman tafiyar price ana kiran su da "Tweezer top" yayin da idan sun bayyana a qasan tafiyar price kuma ana kiran su da "Tweezer bottom" 

    

TWEEZER TOP

Tweezer top tagwayen candles ne daya ja daya kuma kore, suna bayyana ne a karshen tafiyar price yayin da price ke tashi (uptrend). Lokuta dadama candle na farko koren candle (bullish) yana fin jan candle din girma da kadan, gaba dayansu suna fita babu wuya a saman jikinsu amma suna da wutsiya a kasansu (lower shadow).


 Bayyanarsu guda biyun a lokacin da farashi ke tafiya sama alama ce ta canjawar tafiyar farashi, daga tashin farashi zuwa saukar farashi (bearish reversal)

Traders na amfani da bayyanar tweezer top a matsayin alamar dake nuna masu lokacin da ya kamata su sayar da coin ɗinsu kafin farashi ya fara rikitowa. 

TWEEZER BOTTOM 

Su ma tweezer bottom kamar tweezer top su ke, sai dai tweezer bottom suna fita ne a ƙarshen tafiyar price a lokacin da price ke sauka (downtrend). A tweezer top pattern koren candle shi ne ke a farko, 

yayin da a tweezer bottom kuma jan candle shi ne a farko kuma yana fin koren candle ɗin dake binsa girma. Idan sun bayyana a downtrend suna ɗauke da saqo mai qarfi na tashin farashi. 


FOLLOW THIS PAGE FOR FREE SIGNALS AND CRYPTO TRADING KNOWLEDGE FROM BEGINNING TO ADVANCE LEVEL INSHA'ALLAH.

Post by  BRITEC CRYPTO

Download free APK files and Android apps from APK Store. Explore safe, verified, and updated Android applications across multiple categories...

Post a Comment