Stay connected with us Apkstore for Get Latest Update Now. apkstore.com.ng

TECHNICAL ANALYSIS INDICATORS PATTERN   WHAT IS MOVING AVERAGES?

                       


 TECHNICAL ANALYSIS INDICATORS PATTERN 

                                        WHAT IS MOVING AVERAGES?



Yau saikunyi hakuri karatunnamu sai annutsu sosai sabida yanada girma kuma nasan dole zaidaiyi tsayi sabida afahimta yadda yakamata kuma idan naga dayiyiwa kozuwa anjimane zanyimuku dan video akan yadda ake amfani da Moving average insha'allah.

✓✓ Moving average indicator ne da ake amfani da shi wajen gane matsakaiciyar tafiyar da price yayi a lokutan da suka gabata don auna alqiblar da price ke fuskanta a yanzu. Yana daya daga cikin rukunnin 

lagging indicators idan muka koma kara tunmu nabaya watau indicator dake nuni da motsin da price yayi a baya domin fahimtar alkiblar da price ke fuskanta a yanzu.

✓✓ Moving average layine dake ɗauke da siffar tafiyar price na hawa da sauka domin sauƙaƙewa traders fahimtar yadda price ketafiya, kasancewar gane taswirar tafiyar farashi ta hanyar yin duba da bayyanar candles yana da dan rikitarwa. 

✓✓ Moving average tamkar inuwa ne ga trend, suna bin duk motsin da price action watau candlestick pattern yakeyi kamar yadda inuwa ke binka idan kana tafiya da rana. Lokuta dadama mutanen qarnin baya suna amfani da inuwa wajen auna tafiyar lokaci da lokutan sallah. Kamar haka ake amfani da moving averages wajen gane alqibloli da hawa da saukar price: idan trend ya wuce moving average hakan na nufin bullish, idan kuma trend ya yi ƙasa da moving 

averages hakan na nufin bearish

✓✓ Moving average yanayin aiyiki as dynamic support and resistance sannan kuma yanayin aiki as dynamic trend line sabida yana nunamaka hankalin traders yafi karkata.


TYPES OF MOVING AVERAGE 

Moving averages sun kasu kashi biyu: 

1. Simple moving average (SMA) or moving average (MA) 

2. Exponential moving average (EMA)


SIMPLE MOVING AVERAGES 

Wannan nau'in moving average ne dake lissafa adadin closing parice na kowanne candle sannan ya bayar da siffar matsakaiciyar tafiyar da price yayi a lokacin da aka zaba, awaki vedio dazan sak zuwa anjima nasan za'a fuskanci komai insha'allah.

EXPONENTIAL MOVING AVERAGE (EMA

Bambanci da ke tsakanin SMA da EMA sauri ne kawai. EMA ya fi SMA saurin nuna canjawar tafiyar farashi, hakan na nufin da zarar price yafara sauka EMA ne yake fara nunawa, shi kuma SMA yakan yi jinkirin nuna canjawar tafiyar price daya faru yanzu. 

✓✓ Traders na amfani da moving averages domin samun alamomi dayawa akan chart. Suna amfani da alamomin wajen yanke shawarar akan lokaci daya kamata susayi coin (entry) dakuma lokacin daya kamata susayar (exit)

✓✓Akwai alamomi da yawa da traders ke samu ta hanyar amfani da moving averages ga wasu daga ciki: 

● Support and resistance levels 

● Moving average crossovers 

● Price breakouts 

SUPPORT LEVEL 

Support level mataki ne na tafiyar farashi da ke nuna farashin coin ya tsaya bazai cigaba da faɗuwa ba. Idan farashi yasauko zuwa matakin support, yana nuni ne da cewa farashin ya kai maƙurar faɗuwarsa a wannan lokacin, daga nan kuma sai dai ya tashi. 

RESISTANCE LEVEL

Resistance level mataki nena tafiyar price wanda ke nuna price na coin yakai makurar tashinsa a wannan lokacin, daganan saidai yafara saukowa kasa. Idan farashi ya motsa sama harzuwa resistance level to 

alamaceta price zai iya gangarowa. wannan duk bayanine wanda munyishi a karatunnamu nabaya aje aqara dubawa.

PRICE BREAKOUT 

Breakout na faruwa ne idan moving average ya yanka trend watau idan yayanka Candlesticks tasama inanufin idan moving average yana saman chart saiyayi breaking chart yadawo qasa to awannan lokacin trend ya chanza yana nunamaka ankoma uptrend 📈 sannan kuma idan moving average yana qasan trend saiyayi breaking chart taqasa yabullo sama to nanma ansami change na trend yadawo down trend 📉 

MOVING AVERAGE CROSSOVERS 

Crossover na ɗaya daga cikin shaharrun karɓaɓɓun alamomi da traders ke amfani dasu musamman wajen gane lokacin da ya dace susayi coin da lokacin da ya dace su sayar da coin dinsu. 

1: Idan Short-term moving average ya tsallaka long-term moving average yana nuni ne da tashin farashi. Misali, Ɗan kasuwa ya saita moving average guda biyu a chart ɗinsa; na farko ya sanya 50-dayMA, na biyu ya sanya 200-day MA. Idan 50-day MA ( short-term) ya tsallaka 200-day (long-term) hakan alama ce ta farashi zai tashi. 


2: Idan long-term moving average ya tsallaka short-term moving average kuma, hakan na nuni ne da saukar farashi. Misali, Ɗan kasuwa ya saita moving average guda biyu a chart ɗinsa; Na farko ya sanya 50-day MA, na biyu ya sanya 200-day MA. Idan 200-day MA ( short-term) ya tsallaka 50-day (long-term) hakan alama ce ta farashi zai sauka. 

Play ▶️  


✓✓ Akwai video dazan saki akan yadda akeyin amfani da Moving average insha'allah zuwa anjima nasan zakuqara fahimtar yadda yake aiki sosai nagode🙏


FOLLOW THIS PAGE FOR FREE SIGNALS AND CRYPTO TRADING KNOWLEDGE FROM BEGINNING TO ADVANCE LEVEL INSHA'ALLAH

Download free APK files and Android apps from APK Store. Explore safe, verified, and updated Android applications across multiple categories...

Post a Comment