Stay connected with us Apkstore for Get Latest Update Now. apkstore.com.ng

TECHNICAL ANALYSIS: MENENE HAMMER & HANGING-MAN PATTERN

 


               TECHNICAL ANALYSIS CANDLESTICK PATTERNS 

HAMMER & HANGING-MAN PATTERN 

 KAMAR KULLUM YAU ZAMUYI MAGANA AKAN WASU RABE-RABEN CANDLESTICK PATTERNS DA MUKE AMFANI DASU WURIN ANALYSIS MARKET A KASUWAN CRYPTO.

 - DA KUMA YADDA SUKE AMFANI DA AIKIN SU!

 - WADAN-NAN CANDLESTICK PATTERNS DIN SU:-

1- HAMMER PATTERN

2- HANGING-MAN    

1. MENENE HAMMER 🔨PATTERN⤵️



HAMMER CANDLESTICK PATTERN

Mecece Hammer pattern?

Hammer wani candlestick ne dayake bayyana acikin chart, Kalmar "Hammer" kalma ce ta Turanci wadda ke nufin "Guduma" a Hausance. Ana kiran wannan nau'in candle ɗin ne da "Hammer candlestick pattern" sakamakon yana bayyana da siffa irinta guduma

INVERTED HAMMER.

Inverted hammer shima nau'ikan hammer ne dayake bayyana da siffar guduma amman ajuye kai a qasa jelar kuma asama, duka amfanumsu daya da normal hammer mai kai asama

Hammer nau'in candle ne da ke nuni da canjawar tafiyar farashi. Yana bayyana ne a lokacin da prices na coin ke sauka qasa (downtrend), a matsayin alamar da ke nuna cewar ya gama sauka daga nan zai fara tashi sama (uptrend)

Ya kan iya bayyana a jan candle ko kuma koren candle, matuƙar dai ya bayyana a lokacin da farashi ke sauka to ya tabbata hammer ne kuma yana nuni ne da tashin farashi. 

Traders na amfani da bayyanar hammer ne a matsayin lokacin daya kamata su sayi coin. Idan price na sauka sai kuma hammer ta bayyana, to albishir ta ke yiwa trader cewa farashin ya zo maƙurar saukar da zai yi, daga nan kuma zai fara tashi ne kawai. Saboda haka, saisu sayi coin daidai bayyanar hammer ɗin sannan su jira farashin ya tashi sai su sayar su samu riba. 

 - KAMAR YADDA ZAKU GANI A HOTON FARKO DAKE KASAN POST DIN NAN, A HOTON FARKO


-YANA DA [LONG LOWER SHADOW] MAI TSAYI

  -SO WANNAN SHINE HAMMER PATTERN 🟢


- ABINDA HAMMER PATTERNS YAKE FADA MAKA A DUK LOKACIN DA KAGA YA BAYYANA A JERIN CANDLESTICK SHINE, WANNAN KASUWAR ZATA JUYA (REVERSAL) 

IDAN KASUWA TANA [DOWNTREND] 🔴 SAI HAMMER TA BAYYANA HAKAN NA NUNA MAKA CEWA WANNAN KASUWAR ZATA IYA DAGA-WA🚀 TA KOMA [UPTREND] 🟢

           AMMA BABU TABBAS DIN KOMAWAR FA!      

- AMMA AKWAI 90% YAQININ CEWA KASUWAR ZATA IYA JUYA-WA ZUWA UPTREND 📈

- SANNAN KAMAR YADDA ZAKU GANI A CIKIN HOTUNAN DANA DAURA A KASA⤵️

- GA ALAMAR INDA HAMMER TA BAYYANA, A LOKACIN DA KASUWAR TAKE [DOWNTREND] BAYAN HAMMER TA BAYYANA SAI TA JUYA, KASUWAR TA KOMA [UPTREND]📈

- MENENE YASA KASUWAR TA JUYA? SHINE BUYERS SUNFI SELLERS, KARFI A KASUWAR

 [WANNAN SHINE AIKIN HAMMER] DA KUMA AIKIN DA TAKE IDAN TA BAYYANA!



                        2. MENENE HANGING-MAN PATTERN⤵️


                  TECHNICAL ANALYSIS CANDLESTICK PATTERNS 

HAMMER & HANGING-MAN PATTERN 

- KAMAR YADDA ZAKU GANI A HOTO NA 2. DAKE KASAN POST DIN NAN, AKWAI HOTON [HANGING-MAN PATTERNS] DA NA DAURA MAI ALAMAR 🔴


- YANA DA [LONG LOWER SHADOW] SHIMA DAGA KASAN SA⤵️

- SO WANNAN SHINE MUKE KIRA [HANGING-MAN]


- SO KAMAR YADDA NA FADA SHIMA HANGING-MAN OPPOSITE NE NA [HAMMER PATTERNS] A DUK LOKACIN DA KAZO ANALYSIS SAI KAGA [HANGING-MAN] YA BAYYANA A JERIN WANNAN CANDLESTICK DIN NAKA, TO BA KOMAI YAKE NUNA MAKA BA SAI CEWA, 


WANNNA KASUWAR ZATAYI KASA🔴⤵️

- ZATA KARA KASA,📉 DAGA DOWNTREND DA TAKE

- MENENE YA KAWO HAKAN ? HAKAN NA NUNA MAKA SELL SUN FARA DANO KASUWA.

Download free APK files and Android apps from APK Store. Explore safe, verified, and updated Android applications across multiple categories...

Post a Comment