Stay connected with us Apkstore for Get Latest Update Now. apkstore.com.ng

TECHNICAL ANALYSIS: Menene Marubozu a Candlestick Pattern?

                

                 TECHNICAL ANALYSIS CANDLESTICK PETTERNS 


Menene Marubozu a Candlestick Pattern?

Marubozu

Marubozu na daga cikin shahararrun candlestick patterns da ake amfani da su wajen nazarin kasuwanni kamar su hannayen jari (Stocks), Forex, da kuma Crypto.

A takaice, Marubozu fitila ce da ba ta da wick (wato inuwa a sama ko ƙasa), wanda ke nuna cewa farashin bude kasuwa (Open) da rufewa (Close) suna cikin ƙarfin 'yan kasuwa, ba tare da wani jinkiri ba.

Me Ya Sa Aka Kira Shi "Marubozu"?

Marubozu na nufin sanƙo. Candlestick ne da bashi da wick ko kuma yanada ɗan ƙaramin wick. Yana nuna ƙarfin buyers ko sellers idan akayi la'akari da launin sa.

A Hoton farko misalin Bullish 📈 Marubozu ne While Hoto na biyu misalin Bearish 📉 Marubozu 

Rabe-raben Marubozu

1. Bullish 📈 Marubozu:

Wannan nau'in Marubozu yana farawa daga ƙasa (Open) sannan ya tashi zuwa sama (Close) ba tare da wani sauka ba.

Ba shi da lower wick ko kuma upper wick, wanda ke nufin cewa farashin ya tashi ba tare da wani sauka ko jinkiri ba.


Yadda Bullish📈 Marubozu yake aiki a Kasuwa:

Yana nuna ƙarfin masu siye (Buyers) a kasuwa.

Alamar cewa farashin na iya ci gaba da tashi saboda ƙarfin siye ya mamaye masu siyarwa.

Yana tabbatar da uptrend ko kuma yana iya zama farkon bullish reversal (canjin yanayi daga sauka zuwa tashi).


Misali: Idan aka ga Bullish Marubozu a ƙarshen downtrend (saukar farashi), yana iya nuna cewa farashin zai fara tashi.


2. Bearish 📉 Marubozu:


Wannan nau'in Marubozu yana farawa daga sama (Open) sannan ya sauka zuwa ƙasa (Close) ba tare da tashi ba.

Ba shi da upper wick ko kuma lower wick, wanda ke nuna cewa farashin ya sauka ba tare da wani tashi ko jinkiri ba.


Yadda Bearish📉Marubozu yake aiki a Kasuwa:

Yana nuna ƙarfin masu siyarwa (Sellers) a kasuwa.

Alamar cewa farashin na iya ci gaba da sauka saboda ƙarfin siyarwa ya mamaye masu siye.


Yana tabbatar da downtrend 🔴 ko kuma yana iya zama farkon bearish reversal (canjin yanayi daga tashi zuwa sauka).


Misali: Idan aka ga Bearish 📉 Marubozu a ƙarshen uptrend🟢 (tashin farashi), yana iya nuna cewa farashin zai fara sauka.


Yadda Ake Gane Marubozu a Cikin Chart:

1. Bullish 📈 Marubozu:

Jikin fitila mai tsawo da launi mai haske (misali kore ko fari) wanda ke nuna tashi.


Babu wick a ƙasa ko sama.

Open yana ƙasa, Close yana sama.


2. Bearish 📉 Marubozu:

Jikin fitila mai tsawo da launi mai duhu (misali ja ko baƙi) wanda ke nuna sauka.

Babu wick a ƙasa ko sama.

Open yana sama, Close yana ƙasa.

Ma'anar Marubozu a Cikin Yanayin Kasuwa:


1. Bullish 📈 Marubozu:

Idan aka same shi a cikin uptrend🟢, yana tabbatar da cewa tashi zai ci gaba.

Idan aka same shi a ƙarshen downtrend🔴, yana iya zama alamar bullish reversal wato canjin yanayi daga sauka zuwa tashi.


2. Bearish 📉 Marubozu:

Idan aka same shi a cikin downtrend🔴, yana tabbatar da cewa sauka zai ci gaba.

Idan aka same shi a ƙarshen uptrend🟢, yana iya zama alamar bearish reversal wato canjin yanayi daga tashi zuwa sauka.

Baka iya shiga ko fita daga kasuwa kawai dan kaga Marubozu dole kana bukatar yazo a Support ko Resistance level ɗinka ta nan ne zaka nemi confirmation ɗinka na shiga ko fita daga kasuwa 


Support da Resistance Levels:

Idan Bullish 📈 Marubozu ta bayyana a kan support level, yana iya zama lokacin shiga kasuwa (Buy).


Idan Bearish 📉 Marubozu ta bayyana a kan resistance level, yana iya zama lokacin fita daga kasuwa (Sell).


Kada a dogara kacokan akan Marubozu kawai. Ana bukatar a tabbatar da alamar da wasu technical indicators kamar su RSI, MACD, ko Moving Averages.

Bullish 📈 Marubozu: Shiga (Buy) lokacin da aka tabbatar da tashi.


Bearish 📉 Marubozu: Fita (Sell) ko Shiga (Short Sell) lokacin da aka tabbatar da sauka.


Yadda ake amfani da Marubozu a Support da Resistance Levels:


1. Bullish 📈 Marubozu:

Idan kasuwa tana sauka (Downtrend),🔴 sannan aka ga Bullish Marubozu kusa da support level, za a iya yanke shawarar shiga (Buy) domin ana sa ran farashin zai tashi.


2. Bearish📉 Marubozu:


Idan kasuwa tana tashi (Uptrend), 🟢sannan aka ga Bearish Marubozu kusa da resistance level, za a iya fita daga kasuwa (Sell) domin ana sa ran farashin zai fara sauka.

Abubuwan Da Ake Kula Da Su:

Tushen Candlestick: Duba wane yanayi ne Marubozu ta bayyana – a cikin tashi (uptrend) 🟢 ko a cikin sauka (downtrend)🔴.


Girman Candlestick: Tsawon jikin Marubozu na iya nuna ƙarfin motsin kasuwa.


Yanayin Kasuwa: Tabbatarwa da trend lines, support, da resistance levels domin kauce wa ƙarya (fake breakout).

Shawara ta a nan :

Kada a yanke shawara kacokan akan Marubozu kawai; a haɗa da wasu alamomi kamar su volume da momentum indicators.

A duba matsayin kasuwa gaba ɗaya (watau fundamental analysis) don sanin ko akwai wani labari ko abu da zai iya tasiri a farashin.

A takaice dai 

Marubozu na daga cikin mafi aminci da ingantattun candlestick patterns wajen fassara yanayin kasuwa. Ta hanyar fahimtar Bullish da Bearish Marubozu, ana iya hango cigaba ko koma bayan kasuwa. Amma fa, yana da muhimmanci a hada wannan ilimi da sauran dabaru na technical analysis da kuma risk management don samun nasara a ciniki.

In Sha Allahu karatun mu na gaba zamu yi bayani ne akan candlestick "Spinning Tops"

Post by Sir: Sulaiman Haruna Shuraim ✍🏽

Download free APK files and Android apps from APK Store. Explore safe, verified, and updated Android applications across multiple categories...

Post a Comment