TECHNICAL ANALYSIS WHAT IS PIERCING CANDLESTICK PATTERN
Acikin karatunmu dasuka gabata munyi tsallake munmanta under double candlesticks bamuyi bayani akan piercing Candlesticks pattern ba ayimana afuwa.
✓✓ Piercing tagwayen candles ne da ke bayyana a qarshen tafiyar price a lokacin da price ke sauka, bayyanar su alama ce ta canjawar tafiyar
Price daga faduwa ya koma tashi.
✓✓Piercing candlestick patterns na qunshe da candles guda biyu; bullish candle da kuma bearish candle kamar dai yadda dark cloud cover su ke. Bambancin su piercing suna bayyana ne a downtrend yayin da dark cloud cover kuma suna fitowa ne a uptrend,
✓✓ piercing na nuni ne da tashin price yayin da dark cloud cover na nuni ne da saukar price. Bugu da kari, a dark cloud cover pattern koren candle shi ne a farko yayin da a piercing kuma jan candle shi ne a farko.
✓✓Kamar yadda traders ke amfani da bayyanar dark cloud cover a wajen fahimtar lokacin da ya kamata su sayar da coin, haka kuma suna amfani da piercing wajen fahimtar lokacin da ya kamata su sayi coin.
✓✓Lokacin da price na coin ke sauka sai kuma piercing candlestick suka bayyana a karshen tafiyar price, to suna nuni ne da cewa gugun masu saye sun shigo kasuwa kuma suna ta saye har adadin da su ke saye ya rinjayi adadin da a ke sayarwa, saboda haka price zai tashi sosai kamar babu gobe.
FOLLOW THIS PAGE FOR FREE SIGNALS AND CRYPTO TRADING KNOWLEDGE FROM BEGINNING TO ADVANCE LEVEL INSHA'ALLAH.