ENGULFING CANDLESTICK-PATTERN
A yaren Turanci kalmar "Engulfing" na nufin "Fin karfi, yin galaba ko rinjaye" Ana kiran wannan nau'in candles din da "Engulfing candles tick pattern" ne domin suna nuni da rinjayen masu saye akan masu sayarwa ko kuma rinjayen masu sayarwa akan masu saye.
Idan engulfing suka bayyana a tafiyar kasuwa alama ce ta sauyawar tafiyar farashin. Idan farashi sama ya ke yi to bayyanar engulfing nanuni da cewa farashin zai fara sauka. Haka nan idan sun bayyana a lokacin da farashi ya ke sauka, bayyanarsu alamace ta cewa farashin zai tashi.
Engulfing candlestick tagwayen candles ne guda biyu; daya babba, daya kuma qarami. Idan qaramin ya bayyana a jan candle, za ka samu babban kuma ya bayyana a koren candle, idan kuma qaramin ya bayyana kore to za ka samu babban kuma ya fito a jan candle.
TYPES OF ENGULFING CANDLESTICK-PATTERN
Engulfing candlestick pattern ya kasu kashi biyu:
1. Bullish engulfing
2. Bearish engulfing
(1) BULLISH ENGULFING
Bullish engulfing tagwayen candles ne babba da qarami, suna bayyana ne a lokacin da farashi ke sauka (downtrend), bayyanarsu alama ce ta farashi zai canja alqibla daga faduwa qasa zuwa tashi sama.
(2) BEARISH ENGULFING
Bearish engulfing tagwayen candles ne babba da qarami, suna bayyana a lokacin da farashi ke tashi (uptrend) a matsayin alamar da ke nuna saukar farashi sosai na zuwa. A bearish engulfing, qaramin candle din shine kore (bullish) yayin da babban kuma shine ja (bearish), sabanin bullish engulfing da babban ne koren candle shi kuma qaramin ja.
FOLLOW THIS PAGE FOR FREE SIGNALS AND CRYPTO TRADING KNOWLEDGE FROM BEGINNING TO ADVANCE LEVEL INSHA'ALLAH.