SHOOTING STAR CANDLESTICK PATTERN
TECHNICAL ANALYSIS CANDLESTICK PETTERNS
Kamar yadda munkai bayani akan Hammer, Marubozu da Doji akaratunmu dayagabata to shima Shooting star wani nau'in candlestick ne dayake bayyana acikin chats.
Shooting star a siffa tana kama da inverted hammer ta ko wanne ɓangare, amma suna da bambanci ta fuskar sakon da su ke isarwa. Invented hammer na fitowa ne a lokacin da farashi ke sauka(downtrend) yayin da ita kuma shooting star tana fitowa ne a lokacin da farashi ke tashi (uptrend).
Invented hammer na nuni ne da alheri cewa akwai yiyuwar farashi ya daina faɗuwa ya koma yana tashi. Ita kuwa shooting star tauraruwa ce mai wutsiya bayyanar ta ba alheri ba ne domin tana nuni ne da cewa farashi zai koma sauka.
Lokuta dadama shooting star tana fitowa ne jar kala, amma wani lokacin tana fitowa a koriya. Idan ta fito jar kala ta fi bayar da alama mai karfi cewa price zai rikito kasa sosai, idan kuma ta fito a koriya tana bayar da bayani ne akan farashi zai sauka sai da alamar ba ta da karfi sosai, ma'ana ko da farashi ya sauka to ba lallai ya sauka har opening price ba.
Traders suna amfani da bayyanar shooting star a matsayin alamar da ke nuna masu lokacin da ya kamata su sayar da coin idan sun riga sun saya. Idan kuma ba su riga sun saya ba to suna jinkirta saye idan shooting star ta bayyana a uptrend har sai price ya sauka.
Da zarar trader ya sayi coin kuma ya ga price na coin na karuwa zuwa cen kuma ya ga shooting star ta bayyana, to yana yin sauri ya sayar da coin din domin ya sani bayyanar ta alamu ne na price ya gama hawan da zai yi yanzu kuma zai fara sauka.
FOLLOW THIS PAGE FOR CRYPTO TRADING KNOWLEDGE FROM BEGINNING TO ADVANCE LEVEL INSHA'ALLAH.