YADDA ZAKA MAGANCE MATSALAR "YOUR DEVICE ISN'T COMPATIBLE WITH THIS VERSION"
Sau da dama zamuje sauke wani Application daga playstore a wayoyinmu kasancewar version na wayarmu bai kai version na App din ba dazarar mun shiga sai muga "Your Device isn't compatible with this version" ma'ana bazamu iya sauke application din ba kasancewar yayiwa wayarmu girma.
Yadda zaka magance wannan matsalar da farko zaka shiga setting na wayarka sai kaje daga ƙasa zakaga "About Phone" sai ka shiga gun, bayan ya bude sai ka duba "Phone Version" ma'ana version na wayarka.
A misali kaduba kaga wayan version 8 ce, sai kawai ka fito kaje cikin "Chrome" na wayarka ka rubuta sunan app ɗin da kakeso ka sauke da kuma version na wayarka, misali Snapchat V.8.1 , nan take za'a baka na wayarka sai kawai kayi download zakaga ya buɗe normal.
Allah yasa mu dace...