GUZIRIN MAI HAILA:
ABUBUWAN DA LITTAFIN YA KUNSA KAMAR HAKA:
1. GABATARWA
2. BAYANIN JININ AL’ADA ASAUKAKE
3. MATA SUN KASU KASHI HUDU
4. IDAN JINI YANA WASA
5. ABUBUWAN DA HAILA TAKE HANAWA
6. ABINDA MAI HAILA ZATA KULA DASHI
7. ALAMAR DAUKEWAR JININ AL’ADA
8. LOKUTAN DA SALLAH TAKE WAJABA GA MAI HAILA TA RAMA.
9. LITTAFAN DA AKAI NAZARI ACIKIN SU.
1 GABATARWA
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai. Tsira da Amincin Allah sutabbata ga wanda Allah ya saukarawa da ayoyin HAILA, bayan haka.
Dalilin wannan litafi mai suna { GUZIRIN MAI HAILA} shine:
Da yawa daga dalibunmu na Islamiyya dana makarantun matan aure da unguwar zage, da wasu makarantun da nake koyarwa. suna yawan yin tambaya akan jini Al’ada, shine naga ya kamata iniyi karambani domin dalibai su amfana dashi, Ina fatan duk wanda ya mallaki wannan littafi ya amfana dashi to yai min Addu’a kuma duk wanda yaga gyara to ya gyaramin. Allah ya amfanar damu baki daya, saboda {Annabin Rahamaﷺ}. in Allah ya yadda zamu dura a inda aka tsaya a kashi na biyu.
{1} BAYANIN JININ AL’ADA ASAUKAKE
Menene jinin Al’ada? shi dai jinin Al’ada jinine wanda yake fita dan kansa kuma yana fitane daga gaban macen da zata iya daukar ciki kuma ta iya haihuwa wannan shine jinin Al’ada.
Yarda yake:
- Kamarsa: kamarsa dai bakine ko ruwan hanta-hanta.
- Yana da karni: Amma yafi karkata izuwa karnin kifi. amma bai kai karanin kifinba, ko waru, kamar warin danyen nama.
- Yanayin Fitarsa: yana fitane yana izon juna, kamar fitar maniyyi amma shi ba’a jin dadi wajen fitar sa.
- Yanayinsa: Yanayinsa dai mai dumine.
{TAFARKO}
Ita ce wace bata tabayin hailaba, Hukuncinta: zata saurari daukewar jini ne, saboda bata taba yi ba ballantana tasan kwanakin ta, amma ba zatawuce kwana goma shabiyar ba.
{TA BIYU}
Ta biyu itace wacce ta saba yin Al’ada, to Hukuncinsta shine, zata iya kwanakin da ta saba yin Al’ada. Misali : tana yin kwa uku a ko wane wata, to duk wata kwana uku zata yi sai tai wanka tai sallah ta iya saduwa da mijinta.
{TA UKU}
Ita ce mai ciki da akwai magganganun malamai cewar wasu sunce mai ciki tana haila, wasu sunce ba ta yi, to amma zan gina maganartane a kan masu ciki da suke Haila, mai cikin dake haila dai idan cikin yana wata uku zuwa sama to zata iya haila daga kwana daya har zuwa kwana goma shabiyar, idan ya wuce wata shida zata yi haila daga kwana daya har izuwa kwana ishirin ko kwana ishirin da tara.
{TA HUDU}
Ita ce mai istahada shi dai jinin istahada Jane, mai jinin istahada. Hukuncinta kamar macen daba ta yin jini ne. domin wata ta tambayi Manzan rahama (S. A. W.) cewar, tanayin annan jinin har yana zuba da yawa, sai yace: tayi sallah ko da yana zuba akan tabbarmar da take Sallah.
{2} IDAN JINI YANA WASA
Misali mace tana yin haila duk wata kwana uku, amma wani trace ranar juma’a daya. bata yi ranar Asabar ba sai tace Lahadi biyu, bata yi ba ranar litininba sai tace talata uku kuma koda tsallaken kwana nawa yake yi. haka zatayi Lissafinta na Kwanakin da taga jini,
Wani fadin Ance zata kirga da kwana kin da bat yiba.
Amma a maganar bata karfi kamar ta farko. sannan musali idan mace jini yazo mata rana daya a wata, bata sake ganin jini ba har sai bayan kwana takwas, to wanda yazo bayan kwana takwas din to sabuwar haila ce. to amma a wani fadin ance tayi haila amma bata sake ganin jiniba sai bayan kwana Goma sha biyar, to shi jinin da yazo bayan kwana Goma sha biyar ya zama sabuwar haila, wato maganar farko tana nufin indai akwai kwana takwas a tsakanin jinin da wani jini na biyu sabuwar haila.
Amma magana ta biyu tana nufin jinin ya zama bayan daukewar sa akwai kwana goma sha biyar a tsakakani to na biyun sabuwar hailace, wannan maganar ta biyu tafi karfi.
{3} ABUBUWAN DA HAILA TAKE HANAWA SUN KASU KASHI BAKWAI:
- SALLAH: mai haila baza tayi sallah ba. domin Annabin Rahama yace” idan mace tana haila baza tayi sallah ba “. (BUKHARI)
- AZUMI: Idan mace tana haila baza tayi azumi ba amma zata rama bayan jinin ya dauke. Annabin Rahman” “ yana fada in mace tana haila baza tayi azumi ba. (BUKHARI).
- DAWAFI: Mai haila baza tayi dawafi ba domin Annabin Rahama yana cewa” Shi dawafi (kamar) sallah ne sai dai shi anyin magana a cikinsa. (TIRMIZI DARU KHUDNI).
- DAUKAR AL-KUR’ANI MAI GIRMA: Mai haila baza ta taba ko shafar Al-kur’ani ba cikin mafi yawan maganganun Malamai domin Allah yana cewa” SHI Al-kur’ani mai girmane babu mai shafarsa sai masu tsarki. Annabin Rahama yana cewa “Karka shafi Al-kur’ani sai kana da tsarki Amma babu laifi Abuda ta karanta ko tilawa wato karatu da ka batare da rike Al-kur’ani ba.
- SHIGA MASALLACI: Mai haila baza ta shiga masallaciba, saboda Annabin Rahama yana cewa” bazan halartawa mai haila ko janaba shiga masallaci ba. (ABU DAUDA)
- SADUWA: Mai haila mijinta bazai sadu da ita ba saboda Allah yayi hani a cikin Al-kur’ani ‘ inda yake cewa Manzon Allah ( S. A. W.) ” suma tambayarka abisa masu haila to kace musu shi haila cuta ne ku kaucewa mata in suna haila kar ku kusancesu har sai sun sani tsarki.” kuma har sai sunyi wankama za’ a kusancesu.
- SAKI: Baza a saki mace ba in tana haila saboda wata rana Abdullahi dan Umar ya saki matar sa tana haila sai Annabi ya bada umarnin adawo da ita in yaga dama bayan ta gama hailar ya saketa ko ya rike matar sa amma malamai sunce koda mutum ya saki matar sa tana haila to sakin ya zartu wato ta saku.
(5) ALAMAR DAUKEWAR JININ AL’ADA
Alamar daukewar sa dai hanyce biyu ce:
- In mace tasa farin yanki ko auduga ko Toli Fefa (Toilet paper) cikin farjinta ta duba amma bai canja kalaba to tasami tsarki kenan.
- Shine ganin (kassa) abin da ake nufi da kassa shine wani ruwa mai fita daga farji bayan gama jini mai kamar ruwan siminti ko ruwan kobewa, in mace ta ganshi to ta sami tsarki kenan. Amma shi wannan ruwan (ga wace ta saba ne).
(6) LOKUTAN DA SALLAH TAKE WAJABA GA MAI HAILA TA RAMA.
A – Misali idan mace ta sami tsarki kafin rana ta fadi misalin a iya raka’a biyar kafin rana ta fadi ko ace saura minti biyar rana ta fadi ita kuma ta sami tsarki tayi wanka. kuma ya rage minti biyar ko a iya raka’a biyar to zata rama sallar azahar da la’asar.
B- Hakanan idan jini ya dauke kafin alfijir ya keto bayan tayi wanka ya zama za ‘a iya sallah raka’a hudu misalin saura minti hudu alfijir ya keto to zata yi sallar magariba da isha’i.
C- Kuma jini ya dauke bayan tayi wanka ya zama za ‘a iya sallah raka’a uku ko muce bayan tayi wanka saura minti uku alfijir ya keto to zata rama isha ce kawai banda magariba.
(7) LOKUTAN DA BAI WAJABA MAI HAILA TA RAMA SALLAH BA.
a- Idan jini yazowa mace kafin rana ta fadi misalin saura minti biyar rana ta fadi sai jini ya zowa mace to bayan jinin ya dauke mata ba zata rama azahar ba la’asar ba magariba da isha ba.
b-hakanan idan jini yazowa mace kafin alfijr ya keto misalin ace saura minti hudu ya keto sai jini yazo mace baza ta rama magariba da isha ba sai dai indai sakaci tayi sai ta rama.
(8) WANKA
Yadda ake wankan haila kamar wankan janaba yake, kawai sai bambancin niyya, amma niyya a zuci akeyi. ga yadda ake wankan.
Da farko za ‘a samo ruwa mai tsarki kamar yadda aka sani, ruwa mai tsarki shine wanda kamar sa ba canza ba, ko dan – danon sa ko kashin sa. to in an sami wannan ruwa sai kiyi niyya ki fara wanke hannayenki ba a cikin abin wanka ba.
sannan ki wanke gabanki zuwa cinyoyin ki. sai ki wanke kanki sau idan kitson da ake tamke wa da roba ne sai kin warware shi {dole}, saboda ruwa ba zai shiga ba sai kin warware kitson ki. sai kifara wanke bangaren jikin ki na dama sannan na barin hagu shima kamar haka kuma ki kula da matse matsin jikin ki kamar Kasan haba da kasan nono ko tsakiyar cinya ko hammata da dai sauran su sannan ki wanke jikin ki gaba daya sosai. Allah masani.
(9) FA’IDOJI
- Misali idan mace tana hailar kwana uku a wata sai wani watan ya zama tayi kwana ukun bai tsaya ba to sai kara kwana uku a wannan watan, daga haka in bai tsaya ba sai wanka ta cigaba da sallah, amma bazata sake kara ukun ba a wannan watan, domin ya za jinin cuta kenan ba wai ana nufin in ta kara ukun bai tsaya ba tayi ta kara ukun bane a’a in ta kara ukun sau daya shike nan.
- Idan haila ta sami mace a makka tana tsaka da aikin Hajji dukkan komai na aikin hajji za tayi banda dawafi amma in ya zama za’a kwashe su daga makka zuwa kasar su jini kuma bai dauke ba kuma gashi ba tayi dawafin wajibiba to malamai sun ce ta iya shan magani domen jini ya tsaya domin tayi dawafin ta na wajibi.
- Amma idan dawafin farko ne ko kuma dawafin ban kwana to ba bu komai in bata yi ba. Amma ki sani shan magani yana da hadari wannanmma sabo da lurura ne kawai.
- Idan Mace ba ta iya gane yanyin jininta bakine ko ja sai ta zauna tsawo kwana shida ko bakwai wato kwana shida ko bakwai shine kwanaki hailarki duk wata sauran jinin da kike gani zungurar shedan ne yake taba jijiya.
- Idan kuma jinin wataran taga baki wataran taga ja to zata lissafa bakin shine jinin haila.
- Mata su sani in sun sami tsarki zasu wanke gaban su baza ‘a zura dan yatsa ba saboda yana cutarwa kadan daga ciki yana rage jin dadi wajen sasduwa.
- Wasu sun ce mace tana fara haila ne tana’ yar shekara tara har zuwa shekara hamsin, darima yace zata iya haila tana ‘yar shekara tara ko kafin ta kai taran ko bayan shekara hamsin zata iya cigaba da haila ya dangata da yana yinda take ciki ko kasar da take ciki.
وبالله التوفيق