Stay connected with us Apkstore for Get Latest Update Now. apkstore.com.ng

Shugaban mulkin sojin Kasar Gabon Janar Brice Oligui Nguema ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar Asabar .

Da wannan sakamakon, Nguema zai cigaba da zama shugabantar ƙasar bayan shekara biyu yana jagorancinta bayan juyin mulkin da ya hamɓarar da Ali Bongo.

 


Shugaban mulkin sojin Kasar Gabon Janar Brice Oligui Nguema ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata da kashi 90% na kuri'un da aka ƙada

Sakamakon wucin-gadi na zaɓen shugaban ƙasar Gabon ya nuna cewa shugaban riƙo kuma jagoran juyin mulkin ƙasar, Brice Oligui Nguema ne ya lashe zaɓen da kashi 90.35 na ƙuri'u da aka kaɗa, kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gida na ƙasar ta bayyana.


Da wannan sakamakon, Nguema zai cigaba da zama shugabantar ƙasar bayan shekara biyu yana jagorancinta bayan juyin mulkin da ya hamɓarar da Ali Bongo.

"Mr Brice Clotaire Oligui Nguema ya lashe zaɓen shugaban ƙasar bayan samun ƙuri'u mafi rinjaye, inda ya samu ƙuri'a 575,222," in ji ministan harkokin wajen ƙasar, Hermann Immongault.

Wanda ke biye masa shi ne Alain Claude Billie-by-Nze, wanda ya samu kashi 3.02 na ƙuri'un da aka kaɗa.

Dama dai tun kafin zaɓen ake hasashen jagoran gwamnatin sojin ne zai lashe zaɓen, inda masu sukar yanayin zaɓen suke cewa an tsara zaɓen ne ta yadda zai sauƙaƙa masa samun nasara.

Post a Comment