Ɗan majalisar Sarki mafi daɗewa a Masarautar Kano, Abbas Sanusi, ya rasu ya na da shekaru 92.
Marigayi yarima, wanda shi ne Galadiman Kano, muƙami mafi girma a Majalisar Sarki, ya rasu ne a jiya Talata, 1 ga Afrilu, a Kano, bayan ya sha fama da jinya.
Abbas Sanusi, wanda ya taba zama dan Majalisar Masarautar Kano kafin samun ‘yancin kai, mahaifinsa, Sarki Sanusi na daya ya nada shi a matsayin Sarkin Dawakin Tsakar Gida da Hakimin Ungogo a 1959.
Ya zama Dan Iyan Kano a 1962 a zamanin Sarki Muhammadu Inuwa, sannan kuma a zamanin Sarki Ado Bayero ya zama Wamban Kano.
Ya samu matsayi mafi girma na Galadiman Kano a zamanin mulkin dan uwansa Sarki Muhammadu Sanusi II.
An haife shi a 1933 a garin Bichi, inda marigayin ya fara karatunsa a makarantar Elementary ta Kofar Kudu a 1944 kuma ya halarci makarantar Midil ta Kano (Kwalejin Rumfa a yau) a 1948.
Za’ayi Sallar Jana’izarsa a Fadar Sarkin Kano Kofar Kudu, a yau.